Ambaliyar ruwa ya gangara da motoci, ya hallaka mutane da yawa a Abuja

Ambaliyar ruwa ya gangara da motoci, ya hallaka mutane da yawa a Abuja

  • Ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a wani yankin babban birnin tarayya Abuja
  • Rahotanni sun bayyana cewa, ana ci gaba da gano gawarwaki daga yankunan da ruwan sama ya lalata
  • Hukumomi na ci gaba da gudanar da bincike don tabbatar da an ceto wadanda ambaliyar ta rutsa dasu

Abuja - Mutane uku sun mutu a Majalisar Karamar Hukumar Abuja (AMAC) ranar Lahadi 12 ga watan Satumba bayan ambaliyar ruwa.

Ambaliyar, sakamakon ruwan sama, ya sa motoci sun nutse, inda kadarori da dama suka lalace.

Akinfolanre Olowofele, mazaunin Trademore Estate a yankin Lugbe na AMAC, ya bayyana lamarin a matsayin "babban rashi".

Mamakon ruwan sama ya hallaka mutane a babban birnin tarayya Abuja
Motar da ruwan sama ya gangara da ita an ceto ta | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Ya ce kimanin mutane bakwai aka ruwaito sun mutu a yankin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare motar jigon PDP sun yi awon gaba da shi da direbansa

Ya bayyana jaridar TheCable cewa:

“Da misalin karfe 9:30, lokacin ne aka fara ruwan sama. Da misalin karfe 10 na dare, ya dan lafa. Sannan misalin karfe 11 na dare, ruwan ya yi tsanani sosai, ta haka ne ambaliyar ta fara kuma muka fara jin muryoyin mutane suna neman taimako."
"An tsinci gawarwaki shida kuma na sami labarin cewa kauyen da ke bayan wannan - su ma sun samu asarar rayuka a wurin, suna da gawarwaki kusan bakwai da aka tsinto a wurin."

Justine Uwazuruonye, ​​shugaban ayyuka a Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) a Abuja, ta shaida cewa an samu mutane uku da suka mutu a lokacin aikin ceto.

A cewarsa:

“Bala'i matukar gaske. Don haka gidaje da yawa sun cika tare da lalata dukiyoyin mutane. Fiye da komai, an rasa rayuka - rayuka uku a yanzu.
"Mun nemi mazauna garin da su kai rahoto ga 'yan sanda idan suna da wanda ya bace don ci gaba da binciken har zuwa gobe - don kada mu tsayar da binciken.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka fasto a Kaduna, El-Rufai ya yi martani mai zafi

“Muna da ababen hawa da yawa, kusan motoci 15 sun makale a cikin laka. Don haka muna kokarin fitar da motocin. Ya zuwa yanzu, duk masu ruwa da tsaki sun ba da hadin kai.

Wani Sanata ya makale a hanyar Abuja saboda ambaliyar ruwan sama

Wasu sassan babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja zuwa Okene sun kasance cikin ambaliya a ranar Asabar 7 ga watan Agusta wacce ta mamaye su bayan ruwan sama na awa hudu. Daya daga cikin yankunan da abin ya shafa shi ne tsakanin Kwali da Abaji.

Ambaliyar ta sa matafiya sun makale yayin da motoci daga Abuja ba za su iya wucewa zuwa Lokoja, Okene da sassan kudanci ba.

Kimanin motocin bas guda uku ne rahotanni suka ce ambaliyar ta kwashe su. Daga cikin daruruwan matafiya da suka makale har da Sanata daga gundumar Kogi ta yamma, Sanata Smart Adeyemi, inji rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun far ma matafiya, sun yi garkuwa da mutum 5 a Ondo

Adeyemi ya ce:

“Ambaliyar ta yi barna sosai. Na shaida yadda ta yi awon gaba da wasu motoci daga babbar hanya.
”Ni da matafiya da yawa ba za mu iya ci gaba da tafiya ba. Mun makale. Babu wata mafita da ta wuce komawa Abuja.”

Yadda masu tattara shara suka dawowa da tsohuwa N10,287,000 da ta zuba a shara

A wani labarin daban, Wasu dangi a kasar Amurka, Ohio, an ce sun zubar da tsabar kudi $25,000 (N10,287,000) cikin kuskure lokacin da suke taimaka wa kakarsu a aikin tsaftace gida. Wannan ya faru ne a gundumar Lorain in ji rahoto.

An ce dangin sun ci sa’a, wani kamfanin tattara shara ya yi nasarar lalubo shara sannan ya kwaso kudin bayan zubar da kunshin kudin. A cewar ABC News 5, tuni aka mika kudin ga tsohuwa mai kudin.

A cewar Ohio Insider, mai kula da ayyukan tattara sharan, Gary Capan ya ce tawagarsa ta taimaka wa dangin da ba a ambaci sunansu ba wajen gano kudin tsohuwar.

Kara karanta wannan

Jerin manyan jami'an gwamnati 5 da shugaba Buhari ya kora cikin kankanin lokaci

Asali: Legit.ng

Online view pixel