‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da magidanci da iyalinsa 4 a Kaduna sun nemi a biya naira miliyan 20

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da magidanci da iyalinsa 4 a Kaduna sun nemi a biya naira miliyan 20

  • Yan bindigar da suka sace mutane biyar ‘yan gida daya a unguwar Sauri da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna sun tuntubi yan uwansu
  • Maharan sun nemi a biya kudin fansa naira miliyan 20 kafin su sake su
  • Yan bindigar dai sun yi garkuwa da magidanci mai suna Peter Andrew Umoh, matarsa da kuma ‘ya’yansa guda uku

Masu garkuwa da mutanen da suka sace mutane biyar ‘yan gida daya a unguwar Sauri da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna sun bukaci a biya naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa, jaridar Aminiya ta ruwaito.

An rahoto cewa maharan sun kai farmaki yankin ne inda suka yi awon gaba da wani mutum mai suna Peter Andrew Umoh, matarsa da kuma ‘ya’yansa guda uku.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan sanda ke 'tatsar' jama'a kafin su bibiyi miyagun da suka sace 'yan uwansu

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da magidanci da iyalinsa 4 a Kaduna sun nemi a biya naira miliyan 20
‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da magidanci da iyalinsa 4 a Kaduna sun nemi a biya naira miliyan 20 Hoto: The Nation
Asali: UGC

Jaridar Daily Post ta kuma ruwaito cewa tsufa ya tilastawa ‘yan bindigar kyale mahaifin mutumin mai shekaru 86 a duniya.

Sai dai kuma tsohon ya bayyana cewa a kaf danginsa gaba daya babu wanda yake da Naira miliyan 20 da maharan suka bukaci a biya.

ya ce:

“Ina rokon ’yan Najeriya da su taimaka min a ceto ’ya’yana da jikoki.”

Kanwar mutumin da aka yi garkuwa da shi, Misis Josephine Andrew, ta bayyana cewa ’yan bindigar sun ki karbar tayin N300,000 da iyalan suka yi musu.

Ta bayyana suna cikin halin fargabar kada ’yan bindigar su hallaka musu ’yan uwa, don haka tana neman taimakon ’yan Najeriya.

'Yan bindiga sun bindige soja har lahira yayin da suka sace mata da yaranta 2 a Zaria

Kara karanta wannan

A karshe ma’aikatan gonar Obasanjo sun samu ‘yanci bayan kwana 3 a ramin masu garkuwa da mutane

A gefe guda, mun kawo cewa wani lamari mai firgitarwa ya afka Milgoma da ke kallon asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shikan Zaria a jihar Kaduna.

‘Yan bindiga sun isa Milgoma da misalin karfe 9 na daren ranar Litinin kamar yadda mazauna yankin su ka tabbatar.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, sun halaka wani soja sannan suka dauke wata mata da yaranta 2. Kuma sojan ya koma ga mahaliccin sa ne sakamakon ragargazar sa da suka yi da bindigogin su.

Yan bindiga sun sace wani limamin Katolika, sun kashe mutane 11 a jihar Kaduna

A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu 'yan bindiga sun sace wani limamin cocin Katolika a masarautar Ikulu da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin garin, Samuel Kukah, wanda ya tabbatar da harin, ya ce 'yan bindigar sun kai farmaki gidan faston, Rev. Fr Luka Benson, da misalin karfe 7:30 na yammacin ranar Litinin.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun kashe mutum 6, sun yi awon gaba da wasu da dama bayan sun yaudare su da kiran Sallah a Sokoto

Asali: Legit.ng

Online view pixel