'Yan ta'addan Boko Haram sun koma dajin Kaduna – DSS ta ankarar da sauran hukumomi

'Yan ta'addan Boko Haram sun koma dajin Kaduna – DSS ta ankarar da sauran hukumomi

  • DSS ta bukaci hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen sa ido da tattara bayanan sirri saboda shugabannin Boko Haram na yin kaura daga Dajin Sambisa zuwa Kudancin Kaduna
  • An tattaro cewa ’yan ta’addan sun fara yin kaura daga dajin Sambisa da ke Jihar Borno ne zuwa dajin Rijana da ke Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna
  • Rahoto ya nuna cewa babban kwamandan Boko Haram, Ibrahim, tare da tawagarsa na shirin komawa karkashin jagorancin Adamu Yunusu, wanda aka fi sani da Saddiqu

Kaduna - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta nemi hukumomin tsaro a Kaduna da su kasance cikin shirin ko ta kwana kan yiwuwar kai hare-hare, Sahara Reporters ta ruwaito.

Ta bayyana cewa shugabanni da dakarun kungiyar ‘yan ta'adda na Boko Haram sun koma wani daji a Kudancin Kaduna daga Dajin Sambisa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace wani limamin Katolika, sun kashe mutane 11 a jihar Kaduna

'Yan ta'addan Boko Haram sun koma dajin Kaduna – DSS ta ankarar da sauran hukumomi
DSS ta ce 'Yan ta'addan Boko Haram sun koma dajin Kaduna Hoto: The Nation
Asali: UGC

A cikin wata sanarwa da jaridar Peoples Gazette ta gani, an ce yan ta’addan sun kaura daga dajin Sambisa a jihar Borno zuwa dajin Rijana da ke karamar hukumar Chikun ta Kaduna.

Jaridar ta nakalto wani bangare na bayanin yana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wani babban mayakin Boko Haram, Ibrahim (FNU) tare da sojojinsa" suna ƙaura don komawa cikin takwarorinsu" karkashin jagorancin wani Adamu Yunusu (wanda ake kira Saddiqu)".

Don haka, DSS, ta umarci jami’an tsaron Najeriya da jami’an NSCDC da su tsaurara tsaro a yankunan da aka ambata da kuma kewaye, inda ya kara da cewa yakamata ta sanya jami’an ta cikin shiri da bayar da rahoto yadda ya kamata.

A cewar jawabin, “an kuma umurce NSCDC da ta kara sa ido da tattara bayanan sirri a yankunan da aka ambata.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare motar jigon PDP sun yi awon gaba da shi da direbansa

Shugabannin Boko Haram matsorata ne: Tubabben kwamandansu ya tona asiri

A gefe guda, wani tsohon kwamandan ‘yan ta’addan Boko Haram, Adamu Rugurugu, ya ce ya yi watsi da ta’addanci ne sakamakon gano cewa akidar 'yan ta’addan Boko Haram zamba ce.

A cikin bidiyon da PRNigeria ta samu, kasurgumin dan ta'addan ya ce manyan shugabannin kungiyar a koyaushe za su aika su a kashe su ne a fagen daga, tare da yaudarar su cewa aljanna ce za ta zama makomar su idan an kashe su.

A cewar Mista Rugurugu, manyan shugabannin Boko Haram ba sa iya tunkarar sojoji sai dai buya daga baya suna amfani da mayakansu wajen kai hare-haren kan sojoji a arewa maso gabas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng