Yan bindiga sun sace wani limamin Katolika, sun kashe mutane 11 a jihar Kaduna

Yan bindiga sun sace wani limamin Katolika, sun kashe mutane 11 a jihar Kaduna

  • Wasu da ake zaton 'yan bindiga ne sun kai farmaki yankin Ikulu da ke karamar hukumar Zangon Kataf na jihar Kaduna inda suka yi awon gaba da limamin cocin katolika
  • Hakazalika mahara sun kai farmaki kauyen Apiye Jim a masarautar Atyap, duk a karamar hukumar Zango-Kataf inda suka kashe mutane 11
  • Sai dai zuwa yanzu babu wani jawabi daga rundunar 'yan sandan jihar kan haka

Wasu 'yan bindiga sun sace wani limamin cocin Katolika a masarautar Ikulu da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin garin, Samuel Kukah, wanda ya tabbatar da harin, ya ce 'yan bindigar sun kai farmaki gidan faston, Rev. Fr Luka Benson, da misalin karfe 7:30 na yammacin ranar Litinin.

Yan bindiga sun sace wani limamin Katolika, sun kashe mutane 11 a jihar Kaduna
Yan bindiga sun sace wani limamin Katolika, sun kashe mutane 11 a jihar Kaduna Hoto: The Nation
Asali: UGC

Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kaduna, ASP Mohammed Jalige, bai cimma nasara ba saboda bai amsa kira ko amsa sakon tes da aka aiko ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka fasto a Kaduna, El-Rufai ya yi martani mai zafi

A bangare daya kuma, , yan bindiga sun kai mamaya kauyen Apiye Jim a masarautar Atyap, duk a karamar hukumar Zango-Kataf ta Kaduna, inda suka kashe mutane 11.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Harin, a cewar wata majiya, ya faru ne da yammacin ranar Lahadi, 12 ga watan Satumba.

Duk da cewa babu wani tabbaci a hukumance daga gwamnatin jihar ko kuma rundunar 'yan sandan jihar, kakakin kungiyar kudancin Kaduna (SOKAPU), Mista Luka Binniyat, ya tabbatar da harin, jaridar The Cable ta ruwaito.

Binniyat ya ce:

“Gaskiya ne. Sun kuma kashe wani mutum a kauyen Atakshusho kimanin kilomita uku daga wurin da aka fara aikata laifi yayin da suke ja da baya don tserewa.
“Ku tuna cewa an kashe wani Limamin ECWA a wajen garin Zangon Kataf, wanda mutanen mu a ko da yaushe suke kokawa kan ba da mafaka ga masu kisa.

Kara karanta wannan

Coci ya ruguje kan masu bauta ana cikin ibada a Taraba, ya hallaka mutane biyu

“Kamar yadda aka saba, babu wanda aka kama. Muna jiran cikakken bayani kan kisan, bayan haka za mu fitar da sanarwa."

Wata majiya ta ce ba a ga da yawa daga cikin mutanen ƙauyen ba har yanzu bayan harin na Litinin, amma ta lura cewa, ya zuwa yanzu, an gano gawarwakin mutane 11 da suka mutu.

A cewarsa, maharan sun zo da yawa kuma sun aikata laifin cikin tashin hankali.

Ya kara da cewa:

“Su (maharan) sun zo ne lokacin da ake ruwan sama kuma suka raba kansu zuwa kungiyoyi. Sun kai farmaki wasu gidaje kuma da suka gama, sai suka tafi nan take.
“Mutane da yawa na ƙauyen sun ɓace a yanzu. Ba shi yiwuwa mutum ya tantance adadin wadanda suka jikkata har ma da wadanda aka kashe; amma ya zuwa yanzu, na kirga kuma na sami matattu 11 a wurare daban -daban.”

An bankado sabbin mafakar ‘yan bindigar Zamfara da ke tserewa

Kara karanta wannan

Hukumar ICPC ta kwato garkame kadarori da dan majalisar Yobe ya boye na mazabarsa

A wani labari, ‘Yan bindigan da ke aikata ta’asa a Zamfara a halin yanzu suna ta guduwa sakamakon matakan tsaro da gwamnati ta dauka da kuma aikin soji da ke gudana.

Don sanya su cikin damuwa, Gwamnatin Tarayya ta rufe hanyar sadarwar waya yayin da gwamnatin jihar ta rufe wasu kasuwannin da ke aiki a kowane mako.

Ko da yake an sami wasu koma-baya, da yawa sun ce aikin ya cimma nasara sosai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel