'Yan bindiga za su yi mubaya’a idan har aka zaɓi shugaban ƙasa mace a Nigeria, Lauya

'Yan bindiga za su yi mubaya’a idan har aka zaɓi shugaban ƙasa mace a Nigeria, Lauya

  • Yanzu da zaben shugaban kasa na 2023 yake karatowa, kowa ya na ta tofa albarkacin bakin sa dangane da zabin da zai gyara Najeriya
  • Kamar yadda wani lauya mazaunin Abuja ya bayyana nasa ra’ayin, ya ce Najeriya za ta gyaru idan har mace ta shugabance ta
  • Ya bayyana kwararan hujjojin sa da suka sa ya yi wannan furucin a ranar Asabar, ranar da matar sa ta cika shekaru 40 da haihuwa

FCT, Abuja - Dangane da zaben 2023 da ke karatowa, Mr Chuks Akamadu, wani lauya mazaunin Abuja ya bayyana dalilan sa akan yadda shugabancin Najeriya ya dace da mace, idan aka yi la’akari da rawar da mata suke takawa a al’umma

Akamadu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a Abuja, yayin bikin murnar cikar matar sa shekaru 40 a duniya inda yace mace a matsayin shugaban kasa ce kadai zata tsamar da Najeriya daga halin kangin da take ciki, News Wire NGR ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jam'iyyar APC ta fatattaki tsohon gwamna da wasu mambobi 40

'Yan bindiga za su yi mubaya’a idan har aka zaɓi shugaban ƙasa mace a Nigeria, Lauya
'Yan fashin daji. Hoto: News Wire NGR
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lauyan ya ce a shirye yake ya kada wa mace kuri’a a zaben 2023

Lauyan ya ce kuri’arsa ta mace ce mai neman shugabancin kasa a 2023, domin ita kadai ce ta san hanyar da za ta bi wurin kawo gyara dangane da matsalolin Najeriya, rahoton News Wire NGR.

A cewar sa:

“Ina mai tabbatar muku da cewa duk wasu ‘yan bindiga, ‘yan ta’adda da sauran miyagun mutane zasu mika wuya idan mace ta bayar da umarnin hakan.
“Dalilin da ya sa ake fama da rashin tsaro a kasar nan shine rashin bai wa mata damar dakatar da yaran su da mazajen su.
“Idan mace ta zama shugaban kasa, duk wasu masu laifi za su zubar da makamansu su rungumi zaman lafiya, duk inda suke kuwa, za su saurari muryar matan su da iyayen su."

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

Kamar yadda NAN ta ruwaito, ya ce idan aka kalli yanayin siyasar kasar nan, lokaci ya yi da za a bai wa mata damar shugabancin kasar nan, kuma ya bukaci duk wasu ‘yan Najeriya da su mika wuya ga mata don su jagorance su.

Lauyan ya ce mace tana da salo da dabarun canja akalar mulkin kasar nan don samun ci gaba

Akamadu, wanda shine shugaban wata kungiya mai zaman kanta ta CERANY, ya ce yin hakan zai canja alkibilar kasar nan kuma ya kawo sabuwar rayuwa ga ‘yan Najeriya.

“Bari in takaice muku bayani, mata su na da soyayya da tausayi a zukatan su, kuma su na da dabaru iri-iri,” kamar yadda NAN ta ruwaito Akamadu ya ce.

Ya lura da yadda mata suke son aiwatar da ayyuka yadda ya dace yayin da maza suke da girman kan fuskantar komai daki-daki.

Matar sa, Mrs Mich Akamadu ta bayyana farincikin ta da Ubangiji ya nuna mata wannan rana, inda ta kara da cewa tabbas ganin zagayowar haihuwar ka babbar baiwa ce.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 10 da aure, ya gwabje matarsa mai tsohon ciki saboda abinci, ta sheka barzahu

Hotunan mutumin da aka kama ya damfari mutane 64 miliyoyin naira a Kano

A wani rahoton daban, Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani hatsabibin dan damfara bisa zargin sa da amfani da sunan babban bankin Najeriya wurin yasar dukiyar mutane 64 ta hanyar amfani da takardun bogi, LIB ta ruwaito.

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Laraba, 8 ga watan Satumba inda yace an kama wanda ake zargin, Buhari Hassan a Yankaba Quarters ne da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel