A karshe ma’aikatan gonar Obasanjo sun samu ‘yanci bayan kwana 3 a ramin masu garkuwa da mutane

A karshe ma’aikatan gonar Obasanjo sun samu ‘yanci bayan kwana 3 a ramin masu garkuwa da mutane

  • Masu garkuwa da mutane sun sako ma’aikatan gidan gonar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da aka sace
  • An yi garkuwa da ma’aikatan ne a ranar Laraba 8 ga watan Satumba yayin da suke dawowa daga aiki
  • DSP Abimbola Oyeyemi, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, ya ce an ceto ma’aikatan ne a ranar Juma’a 10 ga watan Satumba

Abeokuta, Ogun - Kwanaki uku bayan sace su, rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta ce ta ceto ma’aikatan gidan gonar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo daga ramin masu garkuwa da mutane.

PM News ta ruwaito cewa kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ne ya sanar da hakan a ranar Juma’a, 10 ga watan Satumba.

A karshe ma’aikatan gonar Obasanjo sun samu ‘yanci bayan kwana 3 a ramin masu garkuwa da mutane
A karshe ma’aikatan gonar Obasanjo sun samu ‘yanci bayan kwana 3 a ramin masu garkuwa da mutane Hoto: Nigeria Police.
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa ya bayyana cewa Jami’an da ke yaki da masu yaki da garkuwa da mutanen sun kasance suna bin sawun masu garkuwar, inda ya kara da cewa rundunar ta ci gaba da kakkabe jeji a kewayen yankin tun lokacin da lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

Da dumi dumi: Yan bindiga sun kashe tsohon sarkin da aka dakatar saboda ziyartar Buhari

Oyeyemi ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ee, mun matsawa masu garkuwa da mutanen. Tun jiya (Alhamis) jami’anmu masu yaki da garkuwa da mutane suke cikin daji suna nemansu.
“Sun sami damar gano su cikin daji a bayan Kwalejin Day Waterman, a kan hanyar Kobape. A wannan maraice, sun sake su (wadanda abin ya shafa) ba tare da sun ji rauni ko biyan kudin fansa ba.”

A kan ko an kama, Oyeyemi ya ce “ba a kama su ba tukuna, amma muna da tabbacin za mu yi kamun ba da jimawa ba."

Jaridar Vanguard ta kuma ruwaito cewa an sace ma’aikatan ne da yammacin ranar Laraba 8 ga watan Satumba a kauyen Seseri, yayin da suke dawowa daga aiki.

Ba zama: 'Yan sanda sun ci alwashin kamo wadanda suka sace ma'aikatan Obasanjo

A baya mun kawo cewa, rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta tabbatar da sace ma’aikatan Obasanjo Holdings guda uku da wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka sace su a kan babbar hanyar Kobape zuwa Abeokuta.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun kashe mutum 6, sun yi awon gaba da wasu da dama bayan sun yaudare su da kiran Sallah a Sokoto

The Sun News ta ruwaito cewa kakakin rundunar, Abimbola Oyeyemi ya bayar da tabbacin ne a Abeokuta, yayin tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an sace mutanen ne, a ranar Laraba, 8 ga Satumba, da misalin karfe 6 na yamma, a Kauyen Seseri, kusa da Kobape.

Rundunar ‘yan sandan ta ba da tabbacin cewa jami’an ta za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun ceto ma’aikatan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng