'Yan bindiga sun bindige soja har lahira yayin da suka sace mata da yaranta 2 a Zaria

'Yan bindiga sun bindige soja har lahira yayin da suka sace mata da yaranta 2 a Zaria

  • ‘Yan bindiga sun halaka wani soja yayin da suka afka unguwar Milgoma a Zaria suka yi garkuwa da wata mata da yaranta biyu
  • Duk da dai ba a bayyana asibitin da sojan ya cika ba, amma ya samu miyagun raunuka ne sakamakon ragargazar da ‘yan bindigan su ka yi ma sa
  • Rahotanni sun tabbatar da yadda lamarin ya faru a ranar Litinin, 13 ga watan Satumba da misalin karfe 9 na dare sannan ‘yan bindigan da su ka kai harin sun kai 30

Zaria, Jihar Kaduna - Wani lamari mai firgitarwa ya afka Milgoma da ke kallon asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shikan Zaria a jihar Kaduna.

‘Yan bindiga sun isa Milgoma da misalin karfe 9 na daren ranar Litinin kamar yadda mazauna yankin su ka tabbatar.

Kara karanta wannan

Yadda dakile layin wayoyin GSM ya jawo ‘Yan bindiga suka kai wa Sojoji hari a Zamfara

'Yan bindiga sun halaka wani soja sannan sun yi garkuwa da mata da yaranta 2 a Zaria
'Yan Bindiga. Hoto: The Cable
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, sun halaka wani soja sannan suka dauke wata mata da yaranta 2.

Kuma sojan ya koma ga mahaliccin sa ne sakamakon ragargazar sa da suka yi da bindigogin su.

Wata majiya mai karfi daga Milgoma ta tabbatar da yadda yawan ‘yan bindigan ya kai 30, sannan rike da miyagun makamai suka isa suna harbe-harbe ta ko ina.

Jami’an tsaro sun mayar da harin wanda hakan ne ya janyo suka ragargaji sojan da ya rasa ran sa

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, majiyar ta tabbatar da yadda wasu jami’an tsaro na soji da rundunar ‘yan sanda suka lallabo cikin gaggawa suka fara musu aman wuta, bayan ganin hakan ne ‘yan bindigan ma suka hau ragargazar su wanda hakan ya yi sanadiyyar halaka sojan.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare motar jigon PDP sun yi awon gaba da shi da direbansa

Babu wani rahoto dangane da halaka ‘yan bindigan ko daya har lokacin da Daily Trust ta rubuta rahoton.

Malam Haruna Shika, mazaunin yankin ya ce ‘yan bindiga sun yi garkuwa da yara 6 ne amma jami’an tsaro sun samu nasarar ceto su a Kasuwan Da’a da ke Zaria.

Sai dai mukaddashin jami’in hulda da jama’an rundunar soja ta Zaria, Lt Joy Abah ta ce ba a sanar da ita batun halakar sojan ba.

Wata majiya kuma ta ce mutane 10 ‘yan bindigan su ka yi garkuwa da su amma an samu nasarar ceto su

Wata majiya ta daban daga unguwar ta bayyana yadda masu garkuwa da mutanen suka ajiye daya daga cikin wadanda su ka yi garkuwa dasu sakamakon kasa tafiyar da ya yi.

Sannan majiyar ta ce sun yi garkuwa da mutane 10 ne kafin jami’an tsaro su taimaka wurin sakin su.

Adamawa: Jarumin mai shago ya ragargaji ‘yan daba 2 da su ka yi kokarin fasa masa shago

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan yari, sun saki fursunoni 240 sannan suka kashe sojoji a Kogi

A wani rahoton, kun ji wani mai shago, Mohammed Hamman Adama, ya nuna gwarzontakarsa bayan ya yi dambe da wasu yaran Shila yayin da su ka yi kokarin balle masa shagon sa da ke Sangere Bode a karamar hukumar Yola ta kudu a jihar Adamawa.

LIB ta ruwaito yadda aka tattaro bayanai akan wadanda ake zargin, Umar Sa’ad, mai shekaru 18 da Mohammed Idris, mai shekaru 20 suka lallaba shagon sa da misalin karfe 2:00 na daren 2 ga watan Satumban 2021 da addunan su, gudumomi, sanduna da sauran miyagun makamai.

Bayan isar su shagon har sun fara balle kofar don su samu nasarar yasar shagon. Su na kici-kicin balle kofa mai shagon ya ji kara ya fita cikin sauri.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel