Garin yaba Buhari, gwamnan Imo ya ce Buhari bai damu da muradin mutanen Imo ba

Garin yaba Buhari, gwamnan Imo ya ce Buhari bai damu da muradin mutanen Imo ba

  • Gwamna Hope Uzodinma ya yi kuskure ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari bai damu da muradin mutanen Imo ba
  • An yi imanin cewa gwamnan na Imo ya so ya ce akasin haka ne amma cikin tuntuben harshe ya fadi wani abu daban
  • Ku tuna cewa Buhari ya ziyarci Imo don kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin Uzodimma ta aiwatar

Wani lokaci, mutane sukan yi kuskure kuma su fadi akasin abin da suke so su fadi. Da alama wannan lamarin ne ya faru yayin da Gwamna Hope Uzodimma, yake mayar da martani kan ziyarar Shugaba Muhammadu Buhari kwanan nan a jiharsa.

Gwamnan ya ce shugabannin kudu maso gabas suna goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda "bai mai da hankali" ga muradin mutanen Imo ba.

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

A bayyane yake cewa gwamnan yana kokarin fadin akasin maganarsa ne, watakila yana son yace 'ya mai da hankali' ga muradin mutanen Imo.

Garin yaba Buhari, gwamnan Imo ya ce Buhari bai damu da muradin mutanen Imo ba
Gwamnan Imo ya soki Buhari garin yaba masa | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Da yake magana bayan ziyarar shugaban a gidan talabijin na Channels, Uzodimma ya ce kudu maso gabas na farin ciki da ziyarar shugaba Buhari a yankinsu.

Yace:

"Lokacin da muka fadi haka, muna nufin hakan. Muna nufin kowace kalma da kalma - cewa muna goyon bayan shugaban kasa; muna goyan bayan gwamnatin sa, kuma muna goyon bayan manufofin sa saboda Mista Shugaban ya nuna isasshen sha’awa dangane da tsarin da ya dace wajen sauraro da kuma nuna rashin mai dahankali ga muradun mutanen Imo da Igbo baki daya.”

A bangare guda, kamar yadda aka saba kafafen sada zumunta akan samu martani da dama kan abubuwan da shugabanni suka fada, wannan an samu martani a kafar Facebook.

Kara karanta wannan

Mun yi ta yi wa Buhari addu’o'i amma ba mu ga sakamako ba, inji Sheikh Khalid

Martanin jama'a a kafafen sada zumunta

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin maganganun da mutane ke yi kan maganar gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ga su kamar haka:

Ayanfe Oluwa:

"Ya ce zai yi taka-tsantsan da gayyatarka ta nan gaba kuma ka kyauta ta hanyar gaya masa cewa bai mai da hankali ga mutanen ka ba."

Ezinma Osinachi:

"Ko tunbuben harshe ko tuntuben hanci, an isar da sakon kuma ya zo ta bakin Carmel (sic). Bai mai da hankali ko kadan!"

Godson Udeagha:

"Allah ne ya sa ya furta hakikanin tunaninsa da aikin da yake son yi. Har yanzu ban fahimci dalilin da ya sa wannan mutumin yake da tsanani akan mutanensa ba. Ta yaya Ndi Imo da Ndi Igbo suka yiwa Uzodima laifi?"

Yusuf Adamu:

"Ka kasance mai karanta a matsayin ka na gwamna kana yabon PMB kowane sa'a koda kwa gidan ka yana ci da wuta. Imo na fama da rikici a karkashin kulawar ka. Tattalin arziki yana raguwa ka daina yabon PMB ka kirkiri zauren tattaunawar zaman lafiya da mutanen ka."

Kara karanta wannan

Yan kabilar Igbo ke rike da tattalin arzikin Najeriya, saboda me zasu bar kasar: Shugaba Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel