Ministoci 13 da ya kamata Shugaban kasa Buhari ya fatattaka daga Gwamnatinsa

Ministoci 13 da ya kamata Shugaban kasa Buhari ya fatattaka daga Gwamnatinsa

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya fara yi wa majalisar FEC garambawul
  • Ocherome Nnanna yace akwai wasu Ministocin da ya kamata a fattake su
  • A cikin jerin akwai Godswill Akpabio, Bashir Magashi da Sadiya Farouk

Kwanakin baya shugaba Muhammadu Buhari ya tsige wasu daga cikin Ministocinsa; Ministan noma, Sabo Nanono da Ministan wuta, Saleh Mamman.

Ocherome Nnanna ya yi rubutu a jaridar Vanguard, ya tattaro Ministocin da ya kamata a tsige.

Da farko ya kamata shugaba Muhammadu Buhari ya ajiye kujerarsa da Ministan harkokin man fetur, ya bar wani ya rike mukamin bayan shekaru shida.

Wani Ministan da ya kamata a sauke shi ne Ministan harkokin Neja-Delta, Sanata Godswill Akpabio saboda irin badakalar da ake tafka wa a NDDC.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Hukumar Shige da Fice ta sami sabon shugaba yayin da Babandede ya yi ritaya bayan shekaru 5

A cewar Ocherome Nnanna, tun farko bai kamata a nada Lai Mohammed a matsayin Ministan yada labarai ba, kamata ya yi a bar shi a hedikwatar APC.

Duk da kokarin da yake yi, marubucin ya bada shawarar a fatattaki Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami.

Ministoci
Buhari a taron FEC Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

A kyale Magashi ya zauna da jikokinsa

“A jeri na akwai Ministan tsaro na kasa, Janar Bashir Magashi (mai ritaya). A kyale tsohon sojan ya rika kallon talabijin tare da jikokinsa, aikin me ya yi?”

A halin yanzu ana fama da matsalar rashin tsaro a yankunan Zamfara, Katsina, Kaduna, Neja, Benuwai. A ‘yan kwanakin nan abin har ya kai jihar Filato.

“A sauke Abubakar Malami, babban lauyan gwamnatin tarayya, Ministan shari’a, amma ba za ayi haka ba saboda yana cikin kusoshin gwamnatin Buhari.”

Kara karanta wannan

Buhari: Gwamnan Ebonyi ya yi wa Wike raddi, ya fallasa wadanda suka kawo matsalar tsaro

Ngige da wasu Ministoci 5 sun gaza

“Dole Chris Ngige ya tafi. Adamu Adamu, Dr. Osagie Ehanire, Dr. Ogbonnaya Onu, Zainab Ahmed, da Geoffrey Onyeama ba su da wani amfani.”

Marubucin yace kowa yanzu yana mamakin yadda har yau Sadiya Umar Farouk take kan kujerar Minista.

Zunuban Sabo Nanono a Minista

Kwanaki mun tattaro maku laifuffukan Sabo Nanono, daga ciki ya nemi ya canza shugabannin kungiyar manoma ta AFAN, ya goyi bayan ‘yan taware.

An kuma zargi tsohon Ministan da bada kwangilar Naira miliyan 30 domin a gina masallaci, baya ga N1bn da aka kashe da sunan gyaran ma'aikatar gona.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng