Da Dumi-Dumi: Mutane Sun Yi Asarar Miliyoyin Nairori Yayin da Wata Tankar Man Fetur Ta Kama da Wuta a Yola

Da Dumi-Dumi: Mutane Sun Yi Asarar Miliyoyin Nairori Yayin da Wata Tankar Man Fetur Ta Kama da Wuta a Yola

  • Wata babbar tankar dakon man fetur, ta yi hatsari a Yola, jihar Adamawa, inda lamarin ya haddasa gobara
  • Rahotanni sun bayyana cewa tankar ta fashe ta kama da wuta, yayin da mutane suka yi asarar dukiyoyi masu ɗinbin yawa
  • Wani mutumi da lamarin ya shafa ya bayyana cewa wutar ta cinye shaguna sama da guda 20

Adamawa - Mutane sun yi asarar dukiya ta miliyoyin nairori da sanyin safiyar Litinin a wani lamarin gobara da ya auku a jihar Adamawa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne yayin da wata tankar dakon man fetur, makare da man, ta kama da wuta bayan ta faɗi a shatale-talen Maidoki.

Rahotanni sun nuna cewa babbar motar dakon man fetur ɗin mai lambar rijista YLA 23 XM ta faɗi ƙasa ne yayin da take kokarin shan kwana a kan shatale-talen.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan yari, sun saki fursunoni 240 sannan suka kashe sojoji a Kogi

Mutane Sun Yi Asarar Miliyoyin Nairori a Yola
Da Dumi-Dumi: Mutane Sun Yi Asarar Miliyoyin Nairori Yayin da Wata Tankar Man Fetur Ta Kama da Wuta a Yola Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Shaguna da dama da kuma dukiyoyin mutane sun salwanta sun zama tamkar toka bayan motar ta fashe kuma ta kama da wuta.

Babu wanda ya rasa rayuwarsa sanadiyyar wutar, amma mutane sun rasa dukiyoyin da suka kai kimanin miliyan N35m.

Ya mutane suka ji da lamarin?

Ɗaya daga waɗanda wutar ta yi wa ɓarna, kuma mamallaki wasu dukiyoyi da wutar ta cinye, ya bayyana cewa gobarar ta cinye shaguna sama da 20.

Yace:

"Motoci na guda biyu da kuma kayayyakin aikin mu na kasuwanci wutar ta lalata mana."

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

A halin da ake cikin yanzun, jami'an hukumar kwana-kwana na jihar da kuma jami'an tsaro sun dira wurin domin kai ɗauki kan kiran da aka musu.

Hatsarin ya shafi jeka ka dawo da motoci ke yi a kan hanyar, yayin da direbobin motoci suka tattaru domin babu damar wucewa.

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

A wani labarin kuma Zahra Buhari Ta Aike da Sakon Yabo Ga Mijinta Ahmad Indimi Cikin Soyayya da Tsantsar Kauna

Ɗiyar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari , Zahra Buhari, ta yabawa abokin rayuwarta Ahmad Indimi, cikin soyayya da kauna, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Zahra ta yabawa mijin nata ne kasancewarsa abokin rayuwa nagari na tsawon shekarun da suka shafe tare da juna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel