Yanzu-yanzu: An toshe hanyoyin sadarwa na zamani a jihar Katsina

Yanzu-yanzu: An toshe hanyoyin sadarwa na zamani a jihar Katsina

  • Bayan jita-jita da musu, an toshe layukan sadarwa a jihar Katsina
  • Wannan sabon doka zai shafi kananan hukumomin da matsalar tsaro tayi tsamari ne kadai
  • A baya an kafa sabbon dokokin akalla 11 a wadannan kananan hukumomi

An toshe hanyoyi sadarwa na zamani a kananan hukumomin jihar Katsina akalla 13 a yau Alhamis, 9 ga watan Satumba, 2021.

Wannan sabon abu ba zai rasa alaka da artabun da jami'an tsaro ke yi da yan bindiga a yankin Arewa maso yamma ba.

Kananan hukumomin da wannan abu ya shafa sun hada da Sabuwa, Faskari, Dandume, Batsari, Danmusa, Kankara, Jibia, Safana, Dutsin-Ma da Kurfi, Funtua, Bakori da Malumfashi.

Yanzu-yanzu: An toshe hanyoyin sadarwa na zamani a jihar Katsina
Yanzu-yanzu: An toshe hanyoyin sadarwa na zamani a jihar Katsina
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zamfara: Iyayen daliban da aka sace sun shiga mawuyacin hali bayan katse layukan waya

Iyayen daliban da aka sace daga Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Kaya, karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara, sun koka kan rashin iya jin ta bakin masu garkuwa da mutanen da suka sace 'ya'yansu.

Rundunar ‘yan sanda ta ce an sace dalibai 73 lokacin da 'yan bindiga suka mamaye makarantar da misalin karfe 11 na safiyar Laraba da ta gabata.

Dalibai biyar, dukkansu 'yan mata, sun tsere daga hannun 'yan bindigan ranar Alhamis.

Legit.ng Hausa ta rahoto muku cewa, a ranar Juma’a, Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta umarci kamfanonin sadarwa da su katse sabis na sadarwa a Zamfara - lamarin da ya haifar da rashin sadarwar wayoyin salula a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel