Da duminsa: Dalibai 5 cikin 73 da aka sace a Zamfara jiya sun kubuta

Da duminsa: Dalibai 5 cikin 73 da aka sace a Zamfara jiya sun kubuta

  • Bayan kimanin sa'o'i 24 da sace su, dalibai biyar sun samu kubuta daga hannun yan bindiga
  • Yayinda wasu ke cewa cetosu akayi, wasu rahotanni sun nuna yan bindigan ne suke sakesu
  • Gwamnatin jihar Zamfara ta kulle dukkan makarantun jihar sakamakon wannan hari

Dalibai biyar cikin wadanda aka sace 73 ranar Laraba a makarantar gwamnatin GDSS Kaya, dake karamar hukumar Maradun, jihar Zamfara, sun samu kubuta.

The Punch ta ruwaito cewa tsohon Kansilan gundumar Kaya. Yahaya Kaya, ya tabbatar da kubutar yaran ranar Alhamis.

Yahaya Kaya yace diyarsa, Amina, na cikin wadanda suka samu kubuta daga hannun yan bindigan.

A cewarsa, an mayar da daliban garinsu Kaya, misalin karfe 1 na dare.

Yace suna cikin koshin lafiya.

Kara karanta wannan

Atiku: Ya kamata a kirkiri rundunar 'yan sandan da aikinta shine gadin makarantu

Da duminsa: Dalibai 5 cikin 73 da aka sace a Zamfara jiya sun kubuta
Da duminsa: Dalibai 5 cikin 73 da aka sace a Zamfara jiya sun kubuta
Asali: Twitter

Hukumar yan sanda ta bayyana adadin daliban da aka sace a jihar Zamfara yau

Hukumar yan sandan jihar Zamfara ta bayyana adadin daliban da aka sace a makarantar GDSS Kaya dake karamar hukumar Maradun ta jihar a ranar Laraba.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Muhammadu Shehu, a jawabin da ya saki yace yara 73 yan bindigan suka dauke.

Gwamnatin Zamfara ta sanya dokar ta baci, ta kulle dukkan makarantun jihar

Gwamnatin jihar Zamfara ta sanya dokar ta baci a fadin kananan hukumomi 14 dake jihar.

Hakazalika gwamnatin ta kulle dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu dake dukkan kananan hukumomin jihar.

Wannan ya biyo bayan harin da yan bindiga suka kai garin Kaya, karamar hukumar Maradun ta jihar da dafiyar Laraba inda suka yi awon gaba da daliban makaranta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel