‘Yan banga 5 sun hadu da ajalinsu sakamakon harin ‘yan bindiga a hanyar Birnin Gwari

‘Yan banga 5 sun hadu da ajalinsu sakamakon harin ‘yan bindiga a hanyar Birnin Gwari

  • 'Yan bindiga sun kai wa wasu 'yan banga farmaki inda suka kashe mutum biyar a hanyar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna
  • Lamarin ya afku ne a ranar Talata, 7 ga watan Satumba, a lokacin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga Kaduna
  • Zuwa yanzu ba a ji ta bakin rundunar 'yan sandan jihar ba

Wasu ‘yan bindiga sun halaka ‘yan banga biyar sakamakon bude masu wuta da suka yi a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa wani jigo a yankin, Liman Hussaini Udawa, ya tabbatar da harin inda yace an kai wa yan bangar harin ne a kusa da unguwar Yako da ke hanyar.

‘Yan banga 5 sun hadu da ajalinsu sakamakon harin ‘yan bindiga a hanyar Birnin Gwari
‘Yan banga 5 sun hadu da ajalinsu sakamakon harin ‘yan bindiga a hanyar Birnin Gwari Hoto: Sunnews
Asali: UGC

Ya kara da cewa yan bangar na a hanyarsu ta dawowa daga Kaduna ne lokacin da lamarin ya afku.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: ‘Yan bindiga sun hallaka Mai sarauta, sun dauke mutane a jihar Shugaban kasa

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Maharan sun yi masu kwanton bauna inda suka kona motarsu a kusa da unguwar Yako a kan babbar hanyar. A yanzu haka mun dauko gawarwakin ‘yan bangar su uku.”

Ya kuma bayyana cewa za a binne su a garin Udawa da ke karamar hukumar Chikun ya jihar Kaduna.

Wasu majiyoyi a yankin sun ce an kai wa yan bangar harin ne da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Talata.

Sai dai jaridar ta kuma ruwaito cewa babu wani jawabi daga Kakakin yan sandan jihar, ASP Jalige Mohammed, domin bai amsa kiran waya da sakon tes da aka aika masa ba.

'Yan bindigan da aka fatattaka daga Zamfara sun sace mutum 20 a Sokoto

A wani labari na daban, 'Yan bindigan da ake zargin sun tsere ne daga daga yankunan Bakura - Talata Mafara na jihar Zamfara, a ranar Talata, sun kai hari ƙaramar hukumar Dange Shuni a Sokoto sun sace a ƙalla mutum 20, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tubabbun 'yan bindiga sun koma ruwa, sun shiga hannun 'yan sanda a Katsina

A halin yanzu dai rundunar sojojin Nigeria da wasu hukumomin tsaro suna aikin ragargazar ƴan bindiga a dazukan Zamfara.

Saboda aikin da sojojin ke yi an datse hanyoyin sadarwa na salula da kuma kasuwannin sayar da dabbobi da dakatar da sayar da fetur a jarka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel