Rashin tsaro: Gumi ya yi hasashe mai ban mamaki, ya ce wasu 'yan siyasa sun fi 'yan bindiga ta’asa

Rashin tsaro: Gumi ya yi hasashe mai ban mamaki, ya ce wasu 'yan siyasa sun fi 'yan bindiga ta’asa

  • Shahararren malamin addinin Musulunci da ke zaune a Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi karin haske kan tattaunawar da ya yi da 'yan fashin
  • Gumi ya ce wasu fitattun 'yan Najeriya na yin zagon kasa a kokarin da yake yi na tattaunawa da 'yan bindigar
  • Malamin, ya lura cewa wasu 'yan siyasa sun kashe 'yan Najeriya da basu ji ba basu gani ba fiye da 'yan fashin

Kaduna - Sheikh Ahmed Gumi, fitaccen malamin addinin Islama kuma mai wa'azin addini, ya bayyana cewa wasu 'yan siyasa sun fi 'yan fashi muni saboda illolin almubazarancin da suka yi da albarkatun kasar ya kashe ‘yan Naeriya fiye da' yan fashi.

Legit.ng ta ruwaito cewa Gumi ya bayyana haka ne a wani sharhi da yayi a shafinsa na Facebook mai taken, 'Yaki bai taba zama mafita a ko ina ba, a kowane lokaci.'

Kara karanta wannan

Kai Ɗan Kanzagi Ne, Muƙunshin Gishiri Ka Fi Gishiri Zaƙi, Gumi Ya Yi Wa Kakakin Buhari Wankin Babban Bargo

Rashin tsaro: Gumi ya yi hasashe mai ban mamaki, ya ce wasu 'yan siyasa sun fi 'yan bindiga ta’asa
Rashin tsaro: Gumi ya yi hasashe mai ban mamaki, ya ce wasu 'yan siyasa sun fi 'yan bindiga ta’asa Hoto: Ahmad Gumi.
Asali: Facebook

Ya ce wasu ‘yan Najeriya sun mutu sakamakon cutar kwalara saboda rashin tsaftataccen ruwan sha.

Gumi ya ce:

"Wasu daga cikin 'yan siyasa, wadanda nake kallo a matsayin 'yan fashin birni, saboda illata mana albarkatunmu da suka yi da rashin ba abubuwa muhimmanci, suna haifar da mutuwar mutane da nakasa su fiye da 'yan fashi."

Gumi ya ce wasu masu fada a ji a kasar suna yiwa aikinsa zagon kasa.

Malamin ya ci gaba da bayyana cewa wasu mutane marasa son zaman lafiya sun ce zaman lafiya da tattaunawa da makiyaya da 'yan fashi bai cimma nasara ba.

Kungiyar Oyo ta gargadi sarakunan gargajiya, tana so a binciki ziyarar da Gumi ya kai jihar

A wani labarin, wata kungiya mai zaman kanta mai suna Alliance for Oke-Ogun Development, a yankin Oke-Ogun na jihar Oyo, ta yi kira ga hukumar DSS da ta binciki dalilin ziyarar da Sheikh Ahmad Gumi ya kai garin Igboho.

Kara karanta wannan

Buhari yace yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya yana da matukar wahala

Mai fafutukar Yarbawa, Cif Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho dan asalin garin Igboho ne, hedkwatar karamar hukumar Oorelope ta jihar Oyo.

Jagoran kungiyar ta AOD na kasa, Cif Abiodun Fasasi, a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis ya yi zargin cewa ziyarar Gumi wani yunƙuri ne na mayar da yankin Oke-Ogun na Fulani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel