Jam'iyyar Hammayya PDP Ta Lallasa APC, Ta Lashe Zaben Cike Gurbi a Jihar Delta

Jam'iyyar Hammayya PDP Ta Lallasa APC, Ta Lashe Zaben Cike Gurbi a Jihar Delta

  • Jam'iyyar adawa PDP ta lallasa APC a zaɓen cike gurbi na ɗan majalisar dokokin jihar Delta da aka gudanar ranar Asabar
  • Baturen zaɓe na hukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC, Christopher Onosemuode, ya bayyana ɗan takarar PDP wanda ya lashe zaɓe
  • INEC ta gudanar da wannan zaɓe ne biyo bayan mutuwar tsohon ɗan majalisa a mazaɓar Isoko ta kudu, jihar Delta

Delta - Babbar jam'iyyar adawa People’s Democratic Party, PDP, ta lashe zaɓen cike gurbi na ɗan majalisar dokokin jihar Delta mai wakiltar Isoko ta kudu mazaba ta ɗaya, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Hukumar INEC ta gudanar da zaɓen ne ranar Asabar a baki ɗaya gundumomi 5 na mazaɓar, domin cike gurbin ɗan majalisar yankin, Mr. Kenneth Ogba, wanda ya kwanta dama.

Da yake sanar da sakamakon zaɓen, baturen zaɓen hukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC, Farfesa Christopher Onosemuode, ya bayyana cewa ɗan takarar jam'iyyar PDP, Ovuakpoye Evivie, ya samu kuri'u 6,907.

Kara karanta wannan

Sanatocin Najeriya sun garzaya Landan don gaishe da Tinubu

Jam'iyyar Hammayya PDP Ta Lallasa APC
Jam'iyyar Hammayya PDP Ta Lallasa APC, Ta Lashe Zaben Cike Gurbi a Jihar Delta Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Baturen zaɓen yace ɗan takarar jam'iyyar APC, Dakta Ogaga Ifowodo, ya samu kuri'u 1,301, yayin da ɗan takarar Social Democratic Party, SDP, Mista Emumena Micheal ya sami kuri'u 1,291.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sakamakom zaben cike gurbi a Delta

A jawabin baturen zaɓen yace:

"Ɗan takarar jam'iyyar PDP, Ovuakpoye Evivie, ya samu kuri'u 6,907, yayin da ya samu nasarar kan ɗan takarar APC, Ogaga Ifowodo, wanda ya samu kuri'u 1,301, da kuma na jam'iyyar SDP, Emumena Micheal, mai kuri'u 1,291."

Farfesa Onosemuode ya bayyana ɗan takarar jam'iyyar PDP, Evivie, a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan samun rinjaye a kuri'un da aka kaɗa kuma ya zama zabaɓɓen ɗan majalisa.

A wani labarin kuma tsohon ministan noma da shugaba Buhari ya sallama ya magantu kan irin wahalar da ya sha a ma'aikatar noma

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban kasa ta saki hotunan ziyarar da Buhari ya kai Owerri, jihar Imo

Tsohon ministan noma, Alhaji Muhammad Sabo Nanono, yace jagorantar ma'aikatar noma yana da matukar wahala, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Yace komai yan Najeriya suka kwaso sai ace laifin ma'aikatar noma ne, amma duk da haka mun samu nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel