Gabanin Zaɓen 2023, Bana Bukatar Komawa Matacciyar Jam'iyya, Sanata Ya Soki Yan Siyasa

Gabanin Zaɓen 2023, Bana Bukatar Komawa Matacciyar Jam'iyya, Sanata Ya Soki Yan Siyasa

  • Shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijan Najeriya, Sanata Abaribe, ya gargaɗi yan siyasa kada su koma jam'iyyar APC
  • Sanatan ya faɗi haka ne yayin da yake jawabi a wurin buɗe taron kwamitin zartarwa na PDP karo na 93 a Abuja
  • Yace jam'iyyar APC ita ce ta jefa Najeriya da mutanen dake ciki a halin rashin tsaro da tashin hankali

Abuja - Yayin da ake fuskantar zaɓen 2023, shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai, Enyinnaya Abaribe, ya gargaɗi yan siyasa kada su koma APC, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Sanatan ya bayyana cewa jam'iyyar APC na da hannu a halin da Najeriya take ciki a yanzun.

Sanatan yace:

"Banga dalilin komawa APC ba, domin ita ce jam'iyyar da ta jefa Najeriya halin kakani kayi da ta tsinci kanta yau."

Kara karanta wannan

Babban taro: Majiyoyin PDP sun ce tsofaffin gwamnoni na iya samar da shugaban jam’iyyar na kasa na gaba

Sanata Abaribe
Gabanin Zaɓen 2023, Bana Bukatar Komawa Matacciyar Jam'iyya, Sanata Ya Soki Yan Siyasa Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanatan ya yi wannan magana ne a Abuja, yayin da yake jawabi wurin taron kwamitin zartarwa (NEC) na PDP karo na 93.

Taron ya kunshi dukkanin gwamnoni da suka ɗare madafun iko karkashin jam'iyyar PDP, mambobin kwamitin amintattu BoT, da kuma yan majalisun tarayya.

APC ce ta jefa Najeriya halin da take ciki

A cewar sanata Abaribe, sauya sheka zuwa jam'iyyar APC ba shi da wani amfani, domin jam'iyyar ce ta jefa Najeriya halin da take ciki na rashin tsaro.

Taron NEC ya zo ne awanni 24 bayan gwamnonin PDP sun gudanar da taro kan matsalolin da suka tunnuƙe jam'iyyar PDP.

Bayan taron, shugaban ƙungiyar gwamnonin, Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, yace zasu haɗa kan PDP su lallasa APC a 2023.

Tambuwal ya bayyana cewa gwamnonin zasu haɗa karfi-da-karfe wajen ganin sun kai APC ƙasa domin itace musabbabin halin da ƙasar nan take ciki.

Kara karanta wannan

Sunday Igboho ya ce a mika shi ga Najeriya bai jin tsoron karo da gwamnatin Buhari

A wani labarin kuma Daruruwan yan babbar jam'iyyar adawa PDP sun sauya sheka zuwa APC a hukumance a jihar Osun

Daga cikin waɗanda suka sauya shekar akwai tsohon gwamnan jihar da sauran kusoshin PDP a Osun.

Gwamna Oyetola na jihar Osun tare da shugabannin APC na jiha ne suka karbi sabbin mutanen, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel