Akwai Matukar Wahala Ka Shugabanci Ma'aikatar Noma, Nanono Bayan Buhari Ya Sallame Shi

Akwai Matukar Wahala Ka Shugabanci Ma'aikatar Noma, Nanono Bayan Buhari Ya Sallame Shi

  • Tsohon ministan noma, Alhaji Sabo Nanono, ya bayyana cewa jagorancin ma'aikatar noma yana da wahala sosai
  • Nanono ya faɗi haka ne a wurin taron mika harkokin ma'aikatar ga sabon minista, Dr Mohammad Mahmood Abubakar
  • Yace komai yan Najeriya suka kwaso sai ace laifin ma'aikatar noma ne, amma duk da haka mun samu nasara

Abuja - Tsohon ministan noma, Alhaji Muhammad Sabo Nanono, yace jagorantar ma'aikatar noma yana da matukar wahala, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Ya bayyana cewa ɓangaren masu zaman kansu sun taimaka wajen kalubalen da ya fuskanta.

Nanono ya faɗi haka ne lokacin mika harkokin jagoranci ga sabon minista, Dr Mohammad Mahmood Abubakar, a hedkwatar ma'aikatar dake Abuja.

Tsohon ministan noma, Sabo Nanono
Akwai Matukar Wahala Ka Shugabanci Ma'aikatar Noma, Nanono Bayan Buhari Ya Sallame Shi Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Tsohon ministan yace:

Kara karanta wannan

Jerin manyan jami'an gwamnati 5 da shugaba Buhari ya kora cikin kankanin lokaci

"A wuri na ba abu ne mai sauki ba. Akwai lokutan da zaka samu abu biyo masu karo da juna, a nan da kuma can, amma daga ƙarshe za'a cimma matsaya a fahinci juna."
"Akwai ayyuka da dama da aka ɗora mana a wannan ma'aikatar kuma kowa ya saka mana ido ya ga mai zamu yi."
"Idan aka sami karin farashin kayan abinci, ma'aikatan noma ce, ambaliyar ruwa ma'aikatar noma ce, komai sai ace ma'aikatar noma. Ba damuwa mun yarda aikin mu ne, amma fata na watara wannan ma'aikata ta samu murya ɗaya."

Wane ƙalubale tsohon ministan ya fuskanta?

Tsohon ministan yace ya zo ma'aikatar ne dai dai lokacin da ake fuskantar ƙalubale da suka shafi annobar COVID19, amma duk da haka an yi bakin iya gwargwado.

Hakazalika Nanono ya lissafo wasu nasarori da ya samu da suka haɗa da shirin samar da kayan noma, da kuma kokarin fahintar da shugabn ƙasa ya amince da fitar da biliyan N600bn domin tallafawa kanan manoma.

Kara karanta wannan

Sabon ministan wuta ga 'yan Najeriya: Kada ku yi tsammanin za a samar da wutan lantarki kamar sihiri

A wani labarin kuma Shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijan Najeriya, Sanata Abaribe, ya gargaɗi yan siyasa kada su koma jam'iyyar APC

Sanatan ya faɗi haka ne yayin da yake jawabi a wurin buɗe taron.kwamitin zartarwa na PDP karo na 93 a Abuja.

Yace jam'iyyar APC ita ce ta jefa Najeriya da mutanen dake ciki a halin rashin tsaro da tashin hankali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel