Da dumi dumi: Yan bindiga sun kashe tsohon sarkin da aka dakatar saboda ziyartar Buhari

Da dumi dumi: Yan bindiga sun kashe tsohon sarkin da aka dakatar saboda ziyartar Buhari

  • Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani tsohon sarki a jihar Anambra, Alex Edozieuno a ranar Juma’a, 10 ga watan Satumba
  • Rahotanni sun bayyana cewa an kashe shi ne a Otuocha da ke karamar hukumar Anambra ta gabas na jihar
  • A halin da ake ciki, rundunar 'yan sanda ta tabbatar da kisan kuma tuni jami'an tsaro suka fara bincike

Anambra - Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe wani tsohon sarki a jihar Anambra, Alex Edozieuno, da direbansa, wanda aka bayyana sunansa da Chukwuemeka a ranar Juma’a, 10 ga watan Satumba.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa an yi musu kwanton bauna inda aka kashe su a Otuocha da ke karamar hukumar Anambra ta gabas a jihar da sanyin safiyar Juma’a.

Da dumi dumi: Yan bindiga sun kashe tsohon sarkin da aka dakatar saboda ziyartar Buhari
Yan bindiga sun kashe tsohon sarkin da aka dakatar saboda ziyartar Buhari Hoto: Nigeria police.
Asali: Facebook

Edozieuno yana daga cikin sarakunan gargajiya 12 da gwamnatin jihar Anambra ta sauke kan zuwa Abuja tare da wani Prince Arthur Eze, don ganin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ba tare da izinin gwamnati ba.

Kara karanta wannan

Yadda rikicin Zamfara ya dauko asali shekaru 150 da suka wuce tun kafin zuwan Bature

Jami’in hulda da jama’a na jihar, Ikenga Tochukwu, ya tabbatar da faruwar lamarin, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce Kwamishinan ‘yan sanda, Tony Olofu, ya ba da umarnin bincike kan lamarin.

Kakakin ya ce:

“Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Anambra, Tony Olofu, ya jagoranci tawagar jami’an ‘yan sanda zuwa wurin da aka yi kisan kan a kauyen Ikem Ivife ta gadar Ezu, Otuocha, Anambra ta Gabas.
“Ya bayyana abin da ya faru a matsayin rashin imani kuma ya ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.
“Binciken farko ya nuna cewa yan bindiga sun farma wadanda abin ya rutsa da su, Mista Alex Edozieuno, dan shekara 62, tsohon basaraken karamar hukumar Nkpunado Community Anambra ta Gabas da direbansa Chukwuemeka da misalin karfe 10 na safe a kan gadar Ezu, Otuocha.
“Abubuwan da aka kwato daga wurin sun hada da; Lexus 470 daya tare da lamba No Aguleri-1 mallakar wanda aka kashe da wasu harsasai.

Kara karanta wannan

Nadin Minista: An bayyana Kawu Sumaila da Ahmad a matsayin wadanda ka iya maye gurbin Nanono

“A halin da ake ciki an ajiye gawarwakin a dakin ajiye gawarwaki.
Za a sanar da ƙarin bayani.”

‘Yan bindiga sun kashe mutum 6, sun yi awon gaba da wasu da dama bayan sun yaudare su da kiran Sallah a Sokoto

A wani labarin, mun ji cewa wasu ‘yan bindiga sun halaka mutane shida sannan suka yi garkuwa da wasu da dama bayan sun yaudari mutanen garin Tureta ta jihar Sokoto da kiran Sallar asubahi.

An tattaro cewa ‘yan bindigar na tserewa daga yankin Tureda da ke iyaka da jihar Zamfara sakamakon bude watar da sojoji ke yi, sai dai kuma suna bin kauyuka suna kashe mutane tare da garkuwa da wasu da kuma harbin wasu.

Daily Trust ta kuma ruwaito daga majiya a Tureta cewa da misalin karfe biyun dare, kafin wayewar garin Alhamis, 9 ga watan Satumba, ne ’yan bindigar suka far wa yankin, inda suka yaudari mutane da kiran Sallar asuba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun far ma matafiya, sun yi garkuwa da mutum 5 a Ondo

Asali: Legit.ng

Online view pixel