Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun far ma matafiya, sun yi garkuwa da mutum 5 a Ondo

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun far ma matafiya, sun yi garkuwa da mutum 5 a Ondo

  • 'Yan bindiga sun kai farmaki kan wata motar haya da ke dauke da fasinjoji 18 a kan babbar hanyar Ido Ani-Ifira, jihar Ondo
  • Maharan sun yi garkuwa da mutane biyar a yayin harin wanda ya afku a ranar Laraba, 8 ga watan Satumba
  • Shugaban ‘yan sandan da ke kula da sashen rundunar na Isua Akoko, Mista Hakeem Sadiq, ya tabbatar da faruwar lamarin

Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wata motar kasuwa da ke dauke da fasinjoji 18 a kan babbar hanyar Ido Ani-Ifira, jihar Ondo a yammacin ranar Laraba.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa motar na a hanyar zuwa Abuja daga jihar Legas lokacin da aka kai masu harin.

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun far ma matafiya, sun yi garkuwa da mutum 5 a Ondo
‘Yan bindiga sun far ma matafiya, sun yi garkuwa da mutum 5 a Ondo Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Rahoton ya ce 'yan bindigar sun ja wadanda abin ya shafa cikin daji zuwa inda ba a sani ba.

Kara karanta wannan

Jama’ar gari sun kashe wani da ake zargin dan fashi ne a Katsina

Shugaban ‘yan sandan da ke kula da sashen rundunar na Isua Akoko, Mista Hakeem Sadiq, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce an kai rahoton lamarin, inda ya kara da cewa sashen yaki da garkuwa da mutane na rundunar da sauran hukumomin tsaro suna aiki tukuru don kubutar da matafiyan.

Jama’ar gari sun kashe wani da ake zargin dan fashi ne a Katsina

A wani labarin, mun ji cewa mazauna garin Magama a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina sun yi nasarar kama wani mutum da ake zargi dan fashi ne.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa dan fashin, wanda aka bayyana sunansa a matsayin Baleri, ya badda kamanni don siyan wasu magunguna a cikin garin.

Sai dai kuma, wasu mazauna garin sun gane shi sannan kuma suka far masa, amma a karshe kungiyar 'yan banga ta cece shi inda aka ce sun mika shi ga sojojin da ke sintiri a yankin.

Kara karanta wannan

‘Yan banga 5 sun hadu da ajalinsu sakamakon harin ‘yan bindiga a hanyar Birnin Gwari

Asali: Legit.ng

Online view pixel