Yadda rikicin Zamfara ya dauko asali sama da shekaru 150 da suka wuce tun kafin zuwan Bature

Yadda rikicin Zamfara ya dauko asali sama da shekaru 150 da suka wuce tun kafin zuwan Bature

  • Dr. Murtala A. Rufa’i ya gabatar da takarda a game da rikicin yankin Zamfara
  • Malamin jami’ar ta UDOS yace tun kafin zuwan Turawa ake fama da matsalar
  • Rufa’i ya zargi ‘yan siyasa da Sarakuna da hannu a abubuwan da suke faruwa

Sokoto - Wani malami a jami’ar Usman Danfodiyo da ke garin Sokoto, Dr. Murtala A. Rufa’i, ya dauko sillar kashe-kashen da ake gani yau a jihar Zamfara.

Jami’ar ta gudanar da lacca ta musamman inda Dr. Murtala A. Rufa’i gabatar da takarda a kan binciken da ya yi na tsawon shekaru 10 a dajukan Zamfara.

Daily Trust ta samu labarin abin da yake wakana a wajen wannan laccoci da jami’ar UDUS ta shirya.

Malamin ya bayyana cewa an fara wannan kashe-kashe tun kafin zuwan 'yan mulkin mallaka. Bature ya shigo kasar nan ne kusan shekaru 160 baya.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jami'in dan sanda ya harbe abokin aikinsa dan sanda a jihar Kano

Dr. Murtala A. Rufa’i: Ba yau aka fara ba

“Misali tsaunukan Kwotarkwashi da Tsafe sun kasance mafakar marasa gaskiya, inda suke kitsa danyen aikinsu da ke jawo ayi asarar rayuka da dukiya.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A zamanin mulkin mallaka, akwai lokacin da ‘yan bindiga suka kashe ‘yan kasuwa 210, suka dauke dukiyoyi na £165,000:00."
"Wannan ya faru ne a yankin Zamfara, inda aka kashe wasu mutanen Kano suna hanyar zuwa kasuwancinsu a kasar Faransa.”

Rikicin Zamfara
Sojojin Najeriya a Zamfara Hoto: @Babajide.koladeotitoju
Asali: Facebook

Wannan yanayi na rashin zaman lafiya ya dawo a 2011, yayin da ‘yan bindiga irinsu Kundu da Buharin Daji suka bayyana. Malamin yace dukkansu Fulani ne.

Da farko ‘yan bindigan suna kiran kansu ‘yan gayu, duk da cewa ba matasa ba ne. Rufai yace a 2012 ta’adinsu ya fara bayyana, suka fara satar dabbobin mutane.

Yaushe abubuwa suka ta'azzara?

Kara karanta wannan

Jigon APC ya bayyana wanda ya dace da mulki, ya cire Osinbajo, Tinubu a lissafin 2023

A lokacin da abin ya fara, makiyaya sun soma barin Zamfara saboda karancin wurin kiwo. Sannu a hankali ‘yan bindigan suka fara karfi, har wasu kabilu suka bi su.

A 2012 aka yi wa wani Alhaji Isshe kisan gilla a garin Dansadau, daga nan ba kanta. Masanin yace ‘yan bindigan sun yi karfi da ‘yan kasar waje suka shigo tafiyar.

Jaridar ta rahoto Murtala A. Rufa’i yana cewa akwai inda aka samu wani mai rike da sarautar gargajiya, yana taimaka wa ‘yan bindiga suna yin fashi da makamai.

‘Yan siyasa sun taimaka wa rikicin domin baburan da suke raba wa ake amfani da su a kai hari. Yaran ‘yan siyasan da aka yi watsi da su ne kuma suke shiga harkar.

A bayaninsa, Dr. Rufa’i yace ‘yan bindigan suna samun makamai ne daga kasashen Mali da Libya.

Barazana a Neja-Delta

A makon nan labari ya zo cewa wasu tsofaffin tsagerun Neja-Delta da suka ajiye makamai sun ce a biya su bashin albashinsu ko su fara yin zanga-zanga a yankin.

Kara karanta wannan

NCC: Babu maganar dawo da Twitter yanzu duk Najeriya tayi asarar Naira Biliyan 200

Gwamnati na biyan rsagerun da suka ajiye makamai kudi duk wata, kuma an samu zaman lafiya tun da aka shigo da wannan tsarin a lokacin Ummaru 'Yar'adua.

Asali: Legit.ng

Online view pixel