‘Yan bindiga sun kashe mutum 6, sun yi awon gaba da wasu da dama bayan sun yaudare su da kiran Sallah a Sokoto

‘Yan bindiga sun kashe mutum 6, sun yi awon gaba da wasu da dama bayan sun yaudare su da kiran Sallah a Sokoto

  • 'Yan bindiga sun halaka mutum shida tare da yin garkuwa da wasu da dama a wani hari da ta kai garon Tureta ta jihar Sokoto
  • Maharan sun yaudari mutanen garin ne ta hanyar kiran Sallar asubahi
  • An tattaro cewa bude wutar da sojoji ke wa masu a Jihar Zamfara da ke iyaka da yankin Tureta ne ya tilasta musu tserewa, inda suke bi kauyuka suke ta'asa

Rahoton jaridar Aminiya ya kawo cewa wasu‘yan bindiga sun halaka mutane shida sannan suka yi garkuwa da wasu da dama bayan sun yaudari mutanen garin Tureta ta jihar Sokoto da kiran Sallar asubahi.

An tattaro cewa ‘yan bindigar na tserewa daga yankin Tureda da ke iyaka da jihar Zamfara sakamakon bude watar da sojoji ke yi, sai dai kuma suna bin kauyuka suna kashe mutane tare da garkuwa da wasu da kuma harbin wasu.

Kara karanta wannan

Jama’ar gari sun kashe wani da ake zargin dan fashi ne a Katsina

‘Yan bindiga sun kashe mutum 6, sun yi awon gaba da wasu da dama bayan sun yaudare su da kiran Sallah a Sokoto
‘Yan bindiga sun kashe mutum 6, sun yi awon gaba da wasu da dama bayan sun yaudare su da kiran Sallah a Sokoto Hoto: Punch
Asali: UGC

Daily Trust ta kuma ruwaito daga majiya a Tureta cewa da misalin karfe biyun dare, kafin wayewar garin Alhamis, 9 ga watan Satumba, ne ’yan bindigar suka far wa yankin, inda suka yaudari mutane da kiran Sallar asuba.

Majiyar ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Bayan mutane sun fara fitowa, inda suka zata lokacin sallah ne ya yi, sai kawai ‘yan bindigar suka rika bude musu wuta, sannan suka kashe mutum shida tare da yin awon gaba da wasu.
“Mun tsorata kwarai da gaske, wasunmu ma sun fara kaura zuwa wasu wurare.”

Har ila yau, an tattaro cewa akwai mutane da dama da ’yan bindigar suka harba inda suke karbar magani a asibitin Tureta.

Mataimakin Gwamnan Jihar Sokoto, Maniru Dan’iya, ya ziyarci yankin domin yi musu ta’aziyya a ranar Alhamis, inda ya jaddada aniyar gwamnatin jihar ta ganin bayan ayyukan ’yan bindiga.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke wadanda suka kashe mahaifin tsohon gwamnan Filato

Ya kuma ce gwamnatin za ta dauki nauyin kulawa da wadanda aka kai asibitin.

An toshe hanyoyi sadarwa na zamani a jihar Katsina

A wani laabari na daban, mun kawo cewa an toshe hanyoyi sadarwa na zamani a kananan hukumomin jihar Katsina akalla 13 a yau Alhamis, 9 ga watan Satumba, 2021.

Wannan sabon abu ba zai rasa alaka da artabun da jami'an tsaro ke yi da yan bindiga a yankin Arewa maso gabas ba.

Kananan hukumomin da wannan abu ya shafa sun hada da Sabuwa, Faskari, Dandume, Batsari, Danmusa, Kankara, Jibia, Safana, Dutsin-Ma da Kurfi, Funtua, Bakori da Malumfashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel