Nadin Minista: An bayyana Kawu Sumaila da Ahmad a matsayin wadanda ka iya maye gurbin Nanono

Nadin Minista: An bayyana Kawu Sumaila da Ahmad a matsayin wadanda ka iya maye gurbin Nanono

  • Jama'a sun fara hasashe kan wadanda ka iya maye gurbin ministocin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallama
  • An bayyana Suleiman AbdulRahman wanda aka fi sani da Kawu Sumaila da Ismaeel Buba Ahmed a matsayin wadanda ka iya maye gurbin Nanono daga jihar Kano
  • Shugaban kasar dai ya sallami Sabo Nanono ministan Noma da takwaransa na Wutar Lantarki, Saleh Mamman a ranar 1 ga watan Satumba

Kano - Yayin da kura ke ci gaba da lafawa kan yanayin da ya dabaibaye shawarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari na sallamar ministocinsa guda biyu, hasashe kan wadanda za su iya maye gurbinsu na kara fitowa fili.

Ministoci biyu da aka sauke daga aiki a ranar 1 ga watan Satumba, Sabo Nanono (Noma) da Saleh Mamman (Wutar Lantarki) sun fito ne daga jihohin Kano da Taraba.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan kudu maso gabas ya ce ya yi wuri da za a fara zancen shugabancin Ibo, ya ba da dalili

Nadin Minista: An bayyana Kawu Sumaila da Ahmad a matsayin wadanda ka iya maye gurbin Nanono
Nadin Minista: An bayyana Kawu Sumaila da Ahmad a matsayin wadanda ka iya maye gurbin Nanono Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Tuni ‘yan uwansu suka fara zawarcin gaske don ganin wadanda suka maye gurbinsu sun fito daga jihohinsu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Misali, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Taraba, ta yi kira ga shugaban kasa a bainar jama'a don ganin cewa ba a manta da jihar ba a cikin shirin maye gurbin ministan da aka kora, tare da dora dalilin su kan ba shugaban kasar "sama da 45% na kuri'u yayin zaben shugaban kasa da ya gabata.”

Amma yayin da babu wata kungiya a Kano da ta yi irin wannan rokon, sunaye guda biyu ne a bakunan ‘yan siyasa a jihar a matsayin wanda ka iya maye gurbin Nanono.

Tuni aka fara hasashen Suleiman AbdulRahman (wanda aka fi sani da Kawu Sumaila) tsohon babban mataimaki na musamman ga shugaba Buhari kan harkokin majalisar dokoki na kasa da Ismaeel Buba Ahmed, hadimin Shugaban kasa kan shirin ci gaba a matsayin wadanda za a iya nadawa a matsayin sabbin ministoci daga Kano idan har za a mayar da kujerar jihar.

Kara karanta wannan

Jerin manyan jami'an gwamnati 5 da shugaba Buhari ya kora cikin kankanin lokaci

Bashir Magashi, Ministan Tsaro shine dayan dan majalisar ministoci daga jihar wanda ake yiwa lakabi da bankin kuri’un Buhari.

Kawu Sumaila, dan majalisar wakilai a karo na uku da Ahmed duk mambobin jam’iyyar APC mai mulki ne.

Yayin da ake ta kira ga shugaban kasar da ya tabbatar da ganin cewa an dauki masu fasaha a matsayin wadanda za su maye gurbin mukaman ministocin da ba kowa a kai, manazarta siyasa a Kano sun yi imanin cewa horon da Ahmed ke da shi a matsayin lauya da kuma kuruciyarsa na iya sa shi yin galaba.

A matsayinsa na lauya, sun yi imanin Ahmed zai fi dacewa da Ma’aikatar Muhalli, wanda aka nemi minista ya fara aiki a Ma’aikatar Wutar Lantarki.

Ga Kawu Sumaila, daya daga cikin makusantansa, Alhaji Sule Shuwaki, ya ce kwarewar da ya samu a matsayin dan majalisa da hadimin Shugaba Buhari ya zame masa garkuwa.

Akwai Matukar Wahala Ka Shugabanci Ma'aikatar Noma, Nanono Bayan Buhari Ya Sallame Shi

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta yi nasarar kwato N1trn na kudin sata, Shugabannin APC

A wani labarin, tsohon ministan noma, Alhaji Muhammad Sabo Nanono, yace jagorantar ma'aikatar noma yana da matukar wahala, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Ya bayyana cewa ɓangaren masu zaman kansu sun taimaka wajen kalubalen da ya fuskanta.

Nanono ya faɗi haka ne lokacin mika harkokin jagoranci ga sabon minista, Dr Mohammad Mahmood Abubakar, a hedkwatar ma'aikatar dake Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel