Zaben 2023: Jigon APC ya yi kakkausar gargadi ga shugabannin jam’iyyar mai mulki

Zaben 2023: Jigon APC ya yi kakkausar gargadi ga shugabannin jam’iyyar mai mulki

  • Jigon jam'iyyar APC, Cif Ben Adaji ya gargadi shugabannin jam'iyyar a kan tursasa 'yan takara a zaben 2023
  • Adaji ya ce yin hakan zai kawo hargitsi tare da tarwatsa jam'iyyar
  • Ya kuma yi misali da abun da ya samu babbar siyasar adawar kasar a 2019 wanda ya kai ta ga shan kaye

Taraba - Cif Ben Adaji, jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a Taraba, ya gargadi jam'iyyar game da tursasa 'yan takara da shugabannin jam'iyyar gabanin zaben 2023.

Adaji ya fadi haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Jalingo ranar Alhamis, 9 ga watan Satumba, PM News ta ruwaito.

Zaben 2023: Jigon APC ya yi kakkausar gargadi ga shugabannin jam’iyyar mai mulki
Zaben 2023: Jigon APC ya yi kakkausar gargadi ga shugabannin jam’iyyar mai mulki Hoto: APC
Asali: Facebook

Babban jigon jam’iyyar mai mulki, wanda ya kasance tsohon dan takarar kujerar dan majalisar wakilai ne na mazabar Ankpa, Omala da Olomaboro a Kogi, ya ce abubuwan da suka faru a baya sun nuna cewa yin hakan yana haifar da mummunan sakamako.

Kara karanta wannan

Babbar magana: 'Yan APC sama da 50,000 sun sauya sheka zuwa PDP a Adamawa

Rahoton ya ce Adaji ya lura cewa faduwar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a shekarar 2019, galibi ya faru ne sakamakon tursasa 'yan takara da shugabannin jam'iyyar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya shawarci shugabancin jam’iyyar APC da ta baiwa mambobi damar zabar shuwagabannin su a dukkan matakai tare da kaucewa tursasa ‘yan takarar da basu da farin jini a lokacin zabe.

Adaji ya kuma bukaci APC da ta yi taka tsantsan da wasu mambobin da suka fice daga wasu jam’iyyun siyasa, domin suna iya haifar da matsaloli a jam’iyyar.

Ya ce:

"Muna son APC ta bambanta da PDP a duk gudanarwarta don kayar da PDP.
“Tunda APC ta kwace mulki daga hannun PDP, babbar jam’iyyar siyasa a Afirka, hakan na nufin mutane suna kallon jam’iyyar a matsayin mafi kyawun madadin PDP.

Kara karanta wannan

2023: Wasu manyan jiga-jigan PDP 3 sun sake sauya sheka zuwa APC

“Don haka, dole APC ta yi taka -tsantsan wajen gudanar da dukkan ayyukanta ba tare da nuna son kai da rashin adalci ba.
“Ina ba da shawara ga jami’an jam’iyyar a dukkan matakai da su ba da damar gwabzawa ga masu son yin takara don gwada karfinsu da farin jinin su.”

Tsohon ‘dan takarar Shugaban kasa ya samu matsayi daga sauya-sheka zuwa APC

A wani labarin, tsohon ‘dan takarar shugaban kasa, Gbenga Olawepo-Hashim yana cikin wadanda aka zaba a matsayin wakilan jam’iyyar APC.

Gbenga Olawepo-Hashim ya zama daya daga cikin wakilan jam’iyyar APC na kasa a zaben shugabannin kananan hukumomi da aka yi kwanan nan.

Rahoton yace Olawepo-Hashim zai wakilci mazabar Bwari a babban birnin tarayya Abuja tare da shugaban gunduma, Ali Shere da kuma wasu mutum biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel