Tsohon ‘dan takarar Shugaban kasa ya samu matsayi daga sauya-sheka zuwa APC
- Gbenga Olawepo-Hashim ya shiga cikin wakilan APC a birnin tarayya APC
- An zabi Olawepo-Hashim ne a zaben kananan hukumomin da APC ta shirya
- Sauran shugabannin jam’iyyar na mazabar Bwari sun koma kan kujerunsu
Abuja- The Nation ta ce tsohon ‘dan takarar shugaban kasa, Gbenga Olawepo-Hashim yana cikin wadanda aka zaba a matsayin wakilan jam’iyyar APC.
Gbenga Olawepo-Hashim ya zama daya daga cikin wakilan jam’iyyar APC na kasa a zaben shugabannin kananan hukumomi da aka yi kwanan nan.
Rahoton yace Olawepo-Hashim zai wakilci mazabar Bwari a babban birnin tarayya Abuja tare da shugaban gunduma, Ali Shere da kuma wasu mutum biyu.
An gudanar da wannan zabe ne a WSH Hotel da ke unguwar Bwari a karshen makon da ya wuce.

Kara karanta wannan
Yadda jam’iyyar APC ta tsunduma a rikita-rikita a Jihohi 16 bayan zaben Shugabanni
Gbenga Olawepo-Hashim ya samu mukami a APC
Kamar yadda Daily Trust ta wallafa, dukkanin sauran masu rike da mukamai a jam’iyyar APC a mazabar sun dawo kan mukamansu ba tare da hamayya ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da yake magana bayan an zabe shi a matsayin wakili, Gbenga Olawepo-Hashim ya gode wa ‘ya ‘yan jam’iyyar APC, ya kuma yi kira a ajiye kayan fada.

Source: UGC
‘Dan siyasar ya roki duk masu korafi game da yadda aka gudanar da zaben fitar da gwanin ‘dan takarar shugabannin kananan hukumomi su yi hakuri.
An rahoto Olawepo-Hashim yana yabon wadanda suka zo zaben, kuma ya roki daukacin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC su hada kai a zaben kananan hukumomi.
Wadanda suka halarci wannan zabe sun hada da Hon. Shekwolo Ushafa, Bwari, Idris Umar Farouk, Hon. Adami Ayenajeyi da kuma Hon. Musa Dikko.
Jawabin da Gbenga Olawepo-Hashim ya yi
“Ina rokon fusatattun ‘ya ‘yan jam’iyyar mu mai daraja ta APC, su ajiye kayan fada, su hada-kai, su yi aiki da shugabannin da aka zaba.”

Kara karanta wannan
Jigon APC ya bayyana wanda ya dace da mulki, ya cire Osinbajo, Tinubu a lissafin 2023
“Jimillar karfin tattalin arzikin Najeriya yana bunkasa, ina mai tabbatar maku da cewa APC na aikin kokari domin farfado da tattalin kasa.”
Amaechi/Zulum a 2023?
Kwanan nan aka ji jigon APC, Sanata Alex Kadiri yana fada wa ‘Yan siyasan Arewa, Ibo da na Yarbawa su hakura da neman kujerar shugaban kasa a 2023.
A cewarsa, babu wani ‘Dan siyasan Arewa ta tsakiya da zai iya rike shugaban kasa. Kadiri yana ganin Rotimi Amaechi da Umara Zulum za su iya kai labari.
Asali: Legit.ng