Hotunan lokacin da ministan noma ke zaune a ofis dab da isowar sanarwar korarsa

Hotunan lokacin da ministan noma ke zaune a ofis dab da isowar sanarwar korarsa

  • Bayan da shugaba Buhari ya sallami ministocinsa biyu, kafar sada zumunta ta cika da cece-kuce
  • Legit Hausa ta samo wasu hotuna na daya daga cikin ministocin yayin da yake saurarar dakatar dashi
  • Alamu sun nuna tsohon minista Sabo Nanono kamar a fusace yayin da ake zaman zartarwa

Abuja - A ranar Laraba, 1 ga watan Satumba ne Sabo Nanono ya bar mukaminsa na ministan noma da raya karkara yayin da shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da sallamarsa.

Legit.ng ta tattaro cewa Laraba ita ce ranar karshe ta tsohon minista a ofis yayin da ya shiga taron zartarwa na tarayya (FEC) na mako-mako.

A wani rubutu da aka yada a shafin Facebook na ma'aikatar aikin gona da raya karkara ta tarayya, da alama ministan ya nuna yana cikin bacin rai yayin halartar taron kusan.

Kara karanta wannan

Tunanin halin da yan gudu hijra ke ciki na hanani kuzari lokacin kwanciyar aure: Ortom

Hotunan lokacin ministan gona ke zaune a ofis kafin isowar sanarwar korarsa
Tsohon minista Sabo Nanono | Hoto: Federal Ministry of Agriculture and Rural Development, Nigeria
Asali: Facebook

Wani yankin sanarwar mai dauke da hotunan ministan ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mai Girma Ministan Noma da Raya Karkara, Alh. Muhammad Sabo Nanono, a yau Laraba 1 ga Satumba 2021 ya halarci Babban Taron Zartarwa na Tarayya (FEC)."

Kalli hotunan

Hotunan lokacin ministan gona ke zaune a ofis kafin isowar sanarwar korarsa
Tsohon ministan noma da raya karkara | Hoto: Federal Ministry of Agriculture and Rural Development, Nigeria

Buhari ya kori ministocinsa: Martani da shawarin 'yan Najeriya ga shugaban kasa

Bayan korar ministoci, a wani abin da ya zama abin mamaki ga 'yan Najeriya da yawa ya kuma girgiza su, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 1 ga Satumba ya sallami wasu ministocinsa biyu daga aiki.

A cikin shekaru hudun farko da yayi akan mulki tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019, shugaban ya rike dukkan membobin majalisarsa hannu bibbiyu har zuwa karshen wa'adin mulkinsa na farko.

Mutane da yawa na ganin membobin majalisar Buhari za su ci gaba da kasancewa a mukamansu har zuwa shekakar 2023 lokacin da Buhari zai bar ofis a matsayin shugaban Tarayyar Najeriya.

Kara karanta wannan

Rigingimu 10 da suka jawo Sabo Nanono da Saleh Mamman suka rasa kujerun Ministoci

Sai dai, lamari ya sha bambam, yayin da shugaban, ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Femi Adesina, ya sanar da korar ministan wutar lantarki, Engr. Sale Mamman da na ma’aikatar noma da raya karkara, Mohammed Sabo Nanono.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.