Da duminsa: Miyagu sun sako iyalan Sarkin Kajuru 7 bayan wata 2 da sace su

Da duminsa: Miyagu sun sako iyalan Sarkin Kajuru 7 bayan wata 2 da sace su

  • Masu garkuwa da mutane sun sako mutum bakwai daga cikin iyalan sarkin Kajuru da suka sace kwanakin baya
  • Sun sako mutum bakwai da suka hada da mata 3, maza 3 da karamin yaro daya bayan an biya kudin fansa
  • Sai dai, Dan Iyan Kajuru, Saidu Musa, ya sanar da cewa akwai wasu daga cikin 'ya'ya da jikokin da har yanzu ba a sako ba

Kajuru, Kaduna - Mutum bakwai daga cikin iyalan Alhaji Alhassan Adam, Sarkin Kajuru, sun kubuta daga hannun miyagun masu garkuwa da mutane bayan kwashe watanni biyu a hannun su.

An sako su a ranar Laraba bayan an biya kudin fansa wanda har yanzu ba a bayyana yawan shi ba.

Daga cikin wadanda masu garkuwa da mutanen suka sako, akwai mata uku, maza uku da kuma yaro karami daya, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan bindiga sun gurzu, suna rokon jama'a yafiya tare da sako wadanda suka sace a Zamfara

Da duminsa: Miyagu sun sako iyalan Sarkin Kajuru 7 bayan wata 2 da sace su
Da duminsa: Miyagu sun sako iyalan Sarkin Kajuru 7 bayan wata 2 da sace su
Asali: Original

Daily Trust ta ruwaito yadda miyagun 'yan bindigan suka tsinkayi gidan basaraken a ranar 11 ga watan Yuli kuma suka sace shi tare da wasu mutum 12.

Sai dai, bayan sa'o'i kadan da sace shi aka sako shi.

A yayin tabbatar da sako sauran da aka sace tare da shi, wani mai sarautar Dan Iyan Kajuru, Saidu Musa, ya ce akwai wasu 'ya'ya da jikokin sarkin da har yanzu suke hannun miyagun.

A cikin jama'a basaraken ya fashe da kuka bayan da aka sako shi yayin da jama'arsa suke murnar ganinsa.

Zargin SSS da kutse: Kotu ta yarda da bidiyoyin da aka mika gaban ta a shaidar gidan Igboho

A wani labari na daban, wata babbar kotun da ke zama a Ibadan a ranar Talata ta yarda da bidiyoyin shaida da aka mika gaban ta kan zargin kutsen da jami'an tsaron farin kaya suka yi a gidan Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho a ranar 1 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Zamfara: Iyayen daliban da aka sace sun shiga mawuyacin hali bayan katse layukan waya

Kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa, lauyan Igboho, Yomi Aliyu, SAN, ya mika kara tare da bukatar a biya shi diyyar biliyan N500 daga wurin antoni janar na tarayya, Abubakar Malami, SSS da kuma daraktan DSS na jihar Oyo a kan kutse.

Tun farko Aliyu ya sanar da kotun cewa, an kutsa gidan wanda ya ke karewa da motocinsa kuma an ragargaza tare da kashe wasu mutum biyu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel