Gwamnan arewa ya bayyana dalilin cin hanci da rashawa a Najeriya

Gwamnan arewa ya bayyana dalilin cin hanci da rashawa a Najeriya

  • Gwamna Muhammadu Yahaya ya nuna damuwarsa matuka kan tsarin gudanar da mulkin Najeriya zuwa yanzu
  • Gwamnan na jihar Gombe ya ce rashin kula, sakacin jagorori, da rashin da'a ne suka haifar da ayyukan cin hanci da rashawa a cikin kasar nan
  • Yahaya ya bayyana cewa yana matukar yabawa hangen nesan Shugaban kasa Muhammadu Buhari na tsarkake Najeriya daga cin hanci da rashawa

Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Yahaya, ya ce tarihin cin hanci da rashawa a Najeriya ya ta'allaka ne a kan sakacin jagorori da rashin da'a.

Yahaya ya yi wannan bayanin ne a cikin jawabinsa a ranar Talata, 7 ga watan Satumba, yayin wani taron da Cibiyar Yaki da Cin Hanci da Rasha ta Najeriya ta shirya.

Kara karanta wannan

Kashi 55% na nade-naden da Buhari yayi yan kudancin Najeriya ya baiwa, Hadimin Shugaban kasa

Taron ya kuma samu halartan manyan gwamnati masu rike da mukaman siyasa, jaridar The Punch ta ruwaito.

Gwamnan arewa ya bayyana dalilin cin hanci da rashawa a Najeriya
Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana sakaci a matsayin dalilin cin hanci da rashawa a Najeriya Hoto: Muhammadu Inuwa Yahaya
Asali: Facebook

Yahaya ya yaba wa hangen nesan Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari akan bukatar kawar da cin hanci da rashawa kafin ya durkusar da arzikin kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yahaya ya ce:

“A yau, cin hanci da rashawa ya yi katutu sosai a cikin tsarin rayuwar al’ummar mu. Wannan ya faru ne saboda sakacin gudanarwa na shekaru da dama da rashin da'a.
"Yaki da cin hanci da rashawa yana daya daga cikin manyan manufofin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. Najeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka kan yaki da cin hanci da rashawa.
"Kamar yadda Shugaba Buhari yake cewa: dole ne mu kashe cin hanci da rashawa kafin cin hanci da rashawa ya kashe Najeriya.”

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane sun kashe mace mai juna biyu a Zaria

Fadar shugaban kasa ta yi barazanar hukunta jami'an da aka samu da cin amana

A wani labari, hukumomin fadar shugaban kasa ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wanda ya ci amana da kin sauke hakkokin da aka dora masa yayin gudanar da aikinsa.

The News ta ruwaito cewa sakataren din-din-din na fadar Shugaban kasa, Tijjani Umar ne ya yi wannan gargadin yayin kaddamar da sashin yaki da cin hanci da rashawa na fadar gwamnatin, a ranar Alhamis, 26 ga watan Agusta a Abuja.

Legit.ng ta tattaro cewa Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ce ta kaddamar da sashin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel