Masu garkuwa da mutane sun kashe mace mai juna biyu a Zaria

Masu garkuwa da mutane sun kashe mace mai juna biyu a Zaria

  • Mai martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya koka kan karewar hare-haren yan bindiga a jihar Kaduna
  • Sarkin na Zazzaun na nuna damuwarsa matuka bisa kissar gillar da wasu yan bindiga suka yi wa wata mace mai juna biyu a Zaria
  • Sarkin ya yi wannan jawabin ne yayin da kwamandan hukumar tsaro ta NSCDC na Kaduna, Godwin Miebi ya kai masa ziyara a fadarsa

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya koka kan karuwar harin yan bindiga, yana mai cewa kisar gillar da aka yi wa mace mai juna biyu a Zaria a matsayin abin damuwa.

Daily Trust ta ruwaito cewa sarkin ya ce kasar na cikin wani lokaci mai wahala, yana mai cewa matsalar ba Nigeria kadai ta shafa ba.

Masu garkuwa da mutane sun kashe mace mai juna biyu a Zaria
Taswirar Jihar Kaduna. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan Neja: Dole ne a ilmantar da 'yan Najeriya idan ana son bindiganci ya kare

Matsalar tsaro ba Nigeria kawai ta tsaya ba, Sarkin Zazzau

Ya ce matsala ce da ta karade kasashen duniya don haka ya zama dole dukkan masu ruwa da tsaki su hada hannu don ganin an yi maganin abin a cewar rahoton na Daily Trust.

Ya jadada bukatar hadin kai da aiki tare tsakanin hukumomin tsaro tare da gargadi kan kishi ko kiyayya tsakaninsu.

Sarkin ya yi wannan jawabin ne yayin karbar kwamandan hukumar tsaro da NSCDC reshen jihar, Godwin Miebi, a ranar Alhamis.

Sarkin, ya kuma yabawa hukumar bisa ayyukanta duk da kallubalen rashin isasun kayan aiki da jami'ai.

Abin da shugaban NSCDC ya ce?

A jawabinsa, Miebi ya ce da wahala hukumomin tsaro su samu nasara ba tare da goyon bayan masarautun gargajiya ba.

A cewarsa, don sanin wannan ne yasa ya ziyarci fadan sarkin domin neman goyon bayansa da sauran mambobin majalisarsa kamar yadda aka saba.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da hallaka dan Sanata Bala Na'Allah da aka yi

Ya shaidawa sarkin cewa:

"Muna taka rawar mu wurin hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin ganin an dakile kallubalen rashin tsaro da muke fama da shi a jihar mu."

Tsaro: Gwamnatin Kaduna ta hana yawon gararamba da ayyukan sare itatuwa a dazukan jihar

A wani labarin daban, Gwamnatin Jihar Kana ta haramta yawon 'gararamba' a gari da shiga manyan dazuka a jihar domin yin ayyuka, The Cable ta ruwaito.

Jihar ta kuma hana sare itatuwa domin yin aikin kafinta, girki da gawayi a kananan hukumomi bakwai a jihar saboda karuwar matsalar rashin tsaro.

Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na jihar Samuel Aruwan ne ya bada sanarwar a ranar Talata kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164