Kashi 55% na nade-naden da Buhari yayi yan kudancin Najeriya ya baiwa, Hadimin Shugaban kasa
- Daya daga cikin ma'aikatan fadar shugaban kasa ya bayyana yankin da tafi samin mukamai karkashin mulkin Buhari
- A cewarsa, wasu kullum na kokarin batawa shugaba Buhari suna
- Ngelale ya ce Buhari na iyakan kokarinsa wajen magance matsalar tsaro
Abuja - Babban hadimin shugaban kasa kan lamuran jama'a, Ajuri Ngelale, yace wasu yan Najeriya kullum sun kiran shugaba Muhammadu Buhari da sunan mai nuna kabilanci.
Yayin hira da yan jarida a shirin 'Morning Show' na tashar AriseTV, hadimin shugaban kasan yace ko yaushe ana kokarin ganin Buhari na fifita Arewa.
Ngelale yace duk da soke-soken da ake yiwa Buhari, yana adalci wajen ganin kowa ya samu romin demokradiyya daidai wa daida.
A cewarsa:
"Kun ji labarin cewa an fi baiwa yan Arewa mukaman gwamnatin tarayya karkashin Buhari fiye da sauran sassan Najeriya kuma mutane sun yarda da haka."
"Amma yayinda muka tattara dukkan nade-naden da yayi tun lokacin da ya hau mulki kawo yanzu, mun tarar da cewa kashi 55% na nade-naden gwamnatin nan yan kudu aka baiwa, mafi akasari yankin Kudu maso yamma (Yarbawa)."
Ku Gaggauta Nemo Dabarun Magance Matsalar Tsaron Najeriya, Buhari Ya Umarci Hafsoshin Tsaro
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya umarci shugabannin tsaro su gaggauta nemo hanyoyin warware ƙalubalen tsaro da ya addabi ƙasar nan, musamman a arewa maso yamma da arewa maso tsakiya.
Channels TV ta rahoto cewa Buhari ya bada wannan umarnin ne a fadarsa dake Abuja, yayin taronsa da shugabannin tsaro, wanda ya shafe awanni biyar ranar Talata.
Shugaban ya jaddada bukatar dakile ayyukan yan bindiga, waɗanda a cewar shugabannin tsaron suna kashe al'umma da sace su domin jawo hankalin duniya.
Asali: Legit.ng