Cikin Sauki Sojoji Ke Maganin Yan Bindiga Tun Bayan Datse Sabis Na Sadarwa, Kwamishina

Cikin Sauki Sojoji Ke Maganin Yan Bindiga Tun Bayan Datse Sabis Na Sadarwa, Kwamishina

  • Kwamishinan yaɗa labaru na jihar Zamfara, Ibrahim Dosara, yace tafiyad da ayyukan yan bindiga yazo da sauki
  • A cewar kwamishinan datse hanyoyin sadarwa ya taimaka sosai wajen samun saukin kai hari kan maɓoyar yan ta'addan
  • Yace matakan da gwamnati ta ɗauka ya fara haifar da ɗa mai ido, kuma sojojin ƙasa dana sama suna samun nasara

Zamfara - Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Zamfara, Ibrahim Dosara, yace hare-haren da sojoji ke kaiwa kan yan bindiga ya fara haifar da ɗa mai ido.

Kwamishinan yace abun ya zo da sauki musamman bayan an datshe dukkan hanyoyin sadarwa na jihar.

Dosara ya yi wannan jawabi ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Gusau, ranar Talata, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Ana Samun nasara a Zamfara
Cikin Sauki Sojoji Ke Maganin Yan Bindiga Tun Bayan Datse Sabis Na Sadarwa, Kwamishina Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wane nasarori aka samu zuwa yanzu?

Kara karanta wannan

'Yan bindigan Zamfara 'yan ta'adda ne ba 'yan fashi ba, Cewar Akeredolu

A jawabinsa, Kwamishinan yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A kokarin gwamnatin Zamfara na kawo ƙarshen ayyukan yan bindiga, ta bukaci a katse dukkan sabis ɗin layukan waya na jihar, kuma ta samu haɗin kai nan take."
"Jami'an tsaro sun samu sauki sosai wajen gudanar da aikinsu na magance yan tada ƙayar bayan, har maɓoyarsu dake cikin jeji."

Duk sansanonin yan bindiga da aka sani an tarwatsa su

Kwamishinan ya bayyana cewa duk wasu sansanonin yan bindigan da aka gano, sojojin sama na musu ruwan bama-bamai daga bisani na ƙasa su shiga don karisa waɗanda suka yi kokarin tserewa.

Bugu da kari, Dosara yace gwamnatin Zamfara ta ɗauki wasu matakan na daban dai-dai da irin bayanan sirrin da ta samu.

Wane matakai gwamnati ta ɗauka?

Dorasa yace:

"Daga cikin matakan da muka ɗauka akwai kulle wasu wurare da muke zargin yan bindiga na samun abun amfani."

Kara karanta wannan

Gwamna Masari Zai Katse Hanyoyin Sadarwa a Kananan Hukumomi 3 Na Jihar Katsina

Irin waɗannan wurare sun haɗa da tashoshin mota da suke ba bisa ka'ida ba da kasuwannin kan hanya."

A wani labarin kuma Mijina Ya Haukace, Baya Jimawa a Wurin Kwanciyar Aure, Wata Mata Ta Nemi Kotun Musulunci Ta Raba Aurensu

Wata mata mai suna Lubabatu Ibrahim ta garzaya kotun musulunci a Rigasa Kaduna, ta nemi alkali ya raba ta da mijinta.

Matar tace mijinta ya sami taɓin kwakwalwa, yana ta shi da tsakar dare ya kwalla ƙara kuma ya dinga fatali da komai ya gani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel