Gwamna Masari Zai Katse Hanyoyin Sadarwa a Kananan Hukumomi 3 Na Jihar Katsina
- Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana shirin gwamnatinsa na datse hanyoyin sadarwa a wasu kananan hukumomi
- Masari yace waɗannan matakai da ake ɗauka zasu shafi mutane a hanyar cin abincinsu amma ya zama wajibi
- Gwamnan ya kuma sanar da hana cajin waya a faɗin kananan hukumomi 19 daga cikin 34 dake Katsina
Katsina - Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, yace gwamnatinsa na duba bukatar datse hanyoyin sadarwa a kananan hukumomin Funtua, Bakori da Malumfashi, kamar yadda This Day ta ruwaito.
Gwamnan yace zai ɗauki wannan matakin ne a wani ɓangare na kokarin dakile ayyukan yan bindiga a jihar.
Masari ya bayyana haka ne ranar Litinin, yayin ƙaddamar da kwamitin da zai saka ido kan sabuwar dokar tsaro da gwamnan ya sawa hannu a gidan gwamnati.
Shin dagaske Gwamnatin Katsina ta hana cajin waya?
A wani cigaban kuma, gwamna Masari ya sanar da hana yan kasuwa masu cajin waya a ƙananan hukumomi 19 cikin 34 dake faɗin jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Channels TV ta ruwaito Masari na cewa:
"Muna da yakinin cewa wannan wani ɓangare ne da ke taimakawa yan bindiga wajen samun isasshen sadarwa."
An hana siyar da man fetur a wasu yankuna
Gwamnan yace matakan da gwamnati ke ɗauka ko shakka babu zai shafi kuɗin shigar al'umma amma ya zama wajibi ne a halin yanzu.
Bugu da kari Masari yace waɗannan matakan zasu taimaka wajen hana yan fashi amfani da sabis na sadarwa da wasu abubuwan more rayuwa.
A jawabinsa yace:
"Muna da yakinin cewa da wannan matakin da kuma wanda muke shirin ɗauka tare da ma'aikatar sadarwa zasu taimaka wajen dawo da zaman lafiya a yankin mu."
Bayan Datse Sabis a Zamfara, Gwamnatin Tarayya Ta Yi Magana Kan Datse Sabis Na Sadarwa a Jihar Katsina
"Mun dakatar da siyar da man fetur a Funtua, Bakori da Malumfashi, kuma muna duba yuwuwar datse sauran hanyoyin sadarwa a waɗannan ƙananan hukumomin."
A cewar gwamna Masari, ya kamata mutane su gane cewa babban abokan gaba sune masu baiwa yan ta'addan bayanai saboda haka ya zama wajibi a magance su a sahun farko.
A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Sace 'Ya'yan Basarake Guda Hudu a Jihar Katsina
Wasu miyagun yan bindiga sun yi awon gaba da 'yayan dagacin ƙauyen Sabuwar ƙasa a jihar Katsina.
Harin ya zo awanni 24 kacal bayan wasu mahara sun sace kanwar mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar.
A cewar wani mazaunin ƙauyen, yan bindiga sun kai hari ƙauyen Sabuwar Ƙasa, karamar hukumar Kafur, da safiyar Litinin, inda suka yi awon gaba da ƴaƴan Alhaji Hamza Umar.
Asali: Legit.ng