'Yan bindigan Zamfara 'yan ta'adda ne ba 'yan fashi ba, Cewar Akeredolu
- Gwamna Rotimi Akeredolu ya bayyana 'yan bindigar da ke kai farmaki kan garuruwa daban-daban a jihar Zamfara a matsayin' yan ta'adda
- A cewar gwamnan na jihar Ondo, 'yan bindigar ba 'yan fashi ba ne kamar yadda ake kiran su, sai dai 'yan ta'adda
- Gwamnan ya yi wannan tsokaci ne yayin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga Jami'ar Fasaha ta Tarayya, Akure
Akure - Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, ya ce 'yan bindigar da ake kira 'yan fashi a Zamfara 'yan ta'adda ne, jaridar Punch ta ruwaito.
Akeredolu ya fadi hakan ne a ranar Talata, 7 ga watan Satumba yayin da ya karbi bakuncin mambobin kwamitin gudanarwa na Jami'ar Fasaha ta Tarayya, Akure.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da Legit.ng ta gani kuma kakakin gwamnan, Richard Olatunde ya saki.
An nakalto Akeredolu yana cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Dubi abin da ke faruwa a Zamfara. Suna ƙoƙarin suturta shi sannan kuma suna kiransu 'yan fashi. 'Yan ta'adda ne. Don haka, ci gaban kimiyya ba zai dogara ne akan cajin ku kawai ba illa a kan yanayin da ya dace a ƙasar.”
'Yan ta'adda ba 'yan fashi ba ne'
Hakazalika, Abubakar Bagudu, gwamnan jihar Kebbi ya nuna damuwa kan ayyukan ‘yan fashi da ke haddasa barna a fadin kasar.
Bagudu a ranar Alhamis, 2 ga watan Satumba ya nemi gwamnatin da Buhari ke jagoranta ta ayyana barayin a matsayin 'yan ta'adda.
Magashi: 'Yan fashin daji sun zama fitina, 'yan Najeriya ba su yarda za mu iya maganinsu ba
A wani labarin, Bashir Magashi, ministan tsaro, ya ce 'yan bindiga suna tada hankula a yankunan arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.
TheCable ta ruwaito cewa, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana bukatar a gaggauta magance matsalar su.
Ministan ya sanar da hakan a ranar Talata bayan taron majalisar tsaro da aka yi a fadar shugaban kasa da ke Villa, Abuja.
Asali: Legit.ng