Mijina Ya Haukace, Baya Jimawa a Wurin Kwanciyar Aure, Wata Mata Ta Nemi Kotun Musulunci Ta Raba Aurensu

Mijina Ya Haukace, Baya Jimawa a Wurin Kwanciyar Aure, Wata Mata Ta Nemi Kotun Musulunci Ta Raba Aurensu

  • Wata mata mai suna Lubabatu Ibrahim ta garzaya kotun musulunci a Rigasa Kaduna, ta nemi alkali ya raba ta da mijinta
  • Matar tace mijinta ya sami taɓin kwakwalwa, yana ta shi da tsakar dare ya kwalla ƙara kuma ya dinga fatali da komai ya gani
  • Habibu Ibrahim bai musanta komai ba, amma yace har yanzun yana ƙaunar matarsa, mahifiyar ɗansa

Kaduna - Wata mata yar shekara 25 mai suna Lubabatu Ibrahim, ta bukaci kotun musulunci dake Rigasa ta raba aurenta da Habibu Ibrahim domin ba shi da cikakkiyar lafiyar kwakwalwa, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Matar wacce ta shigar da ƙara gaban kotun, ta bayyana cewa aurensu ya samu albarkar samun ɗa guda ɗaya.

Lubabatu ta shaidawa kotun cewa wanda take kara yana fama da ciwon kwakwalwa kuma yana tashi da tsakar dare ya kwalla ƙara, sannan duk abinda yazo gabansa zai yi fatali da shi.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi: Tura sojoji su ragargaji 'yan bindiga ba zai magance rashin tsaro ba

Wata mata ta nemi kotun musulunci ta raba aurenta da mijinta
Mijina Ya Haukace, Baya Jimawa a Wurin Kwanciyar Aure, Wata Mata Ta Nemi Kotun Musulunci Ta Raba Aurensu Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Lubabatu tace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sannan kuma ba ya iya jimawa a wurin saduwar aure, kwata-kwata ba ya iya wuce minti 2 kacal."
"Na ba shi shawara ya nemi magani a wurin likitoci amma sam ya ki daukar shawarar da na ba shi."

Shin dagaske mijin yana fama da wannan lalura?

A ɓangarensa, wanda ake ƙara Habibu Ibrahim, bai musanta ko ɗaya daga cikin bayanan da matarsa ta gabatar wa kotu ba.

Amma ya ƙara da cewa yana neman taimakon masana lafiya a asibitin masu taɓin hankali kuma yana shan magungunan gargajiya game da matsalar rashin jimawa wajen kwanciyar aure.

Inason matata, ban shirya sakinta ba

Malam Habibu ya shaidawa alkalin kotun cewa har yanzun yana ƙaunar matarsa kuma baya son rabuwa da ita a yanzun.

Alkalin kotun, mai shari'a Malam Salisu Abubakar Tureta, ya umarci ma'auratan biyu da su zo da waɗanda zasu tsaya musu ranar 21 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Sace dalibai 73 a Zamfara: ACF ta dau zafi, ta ce duk gwamnatin da ba za ta kare al’umma ba bata da amfani

A wani labarin kuma Buhari Ya Gode Mana Bisa Kokarin da Muke Yi, IGP Ya Magantu Bayan Taron Tsaro a Aso Villa

Sufeta Janar na rundunar yan sandan Ƙasar nan, Usman Baba, yace Buhari ya yabawa shugabannin tsaro bisa kokarin da suke yi, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

IGP ya bayyana cewa shugaban ya umarci a ƙara zage dantse domin kawo karshen kalubalen tsaron da ya addabi ƙasa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel