Gwamnatin jihar Imo na shirin tarbar shugaba Buhari, inji kwamishina
- Yanzu haka an shirya komai don ziyarar shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa jihar Imo a ranar Alhamis, 9 ga watan Satumba
- Yayin ziyarar tasa, shugaban kasar zai kaddamar da manyan ayyuka da gwamnatin da Hope Uzodimma ke jagoranta tayi
- Jami'an gwamnatin jihar sun ce a shirye suke su tarbi shugaban kasar, yayin da ake ci gaba da kokarin ganin ziyarar ta zama ta tarihi
Owerri - Kwamishinan yada labarai na Imo, Declan Emelumba, ya ce gwamnatin jihar na shirin tarbar shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 9 ga watan Satumba a Owerri.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ba da rahoton cewa an shirya shugaban kasar zai kai ziyarar aiki zuwa Imo don kaddamar da wasu ayyukan da jihar ta aiwatar.
Emelumba ya ce shugaban zai kaddamar da muhimman ayyukan da Gwamna Hope Uzodimma ya fara a cikin watanni 18 da suka gabata.
Kalamansa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Mun shirya sosai don karbar bakuncin Shugaban kasa a Imo. An kammala duk wasu shirye-shirye.
"Da isowarsa, ana sa ran zai fara kaddamar da ayyuka, ciki har da hanyar Naze-Nekede-Ihiagwa-Obinze da titin karkashin kasa akan hanyar D-Tiger Owerri."
Ya ce Buhari zai kuma kaddamar da titin Egbeada da sabbin dakunan majalisar zartarwa na jihar a gidan gwamnati, da sauran su.
Ya kara da cewa:
"Ziyarar tasa za ta baiwa 'yan Imo damar gani da maraba da shugaban kasar."
Tuni, babban birnin jihar, Owerri, ya riga ya dauki sabon salo, musamman kan manyan hanyoyin da ke sada mutum da wuraren ayyukan da za a kaddamar.
Ana sake gina titin da ke gaban Gidan Gwamnati, ana gyara manyan hanyoyi da kuma share su.
Jaridar Guardian ta rahoto cewa gwamnatin jihar Imo ta rufe bankunan da dama a jihar saboda bin umurnin da kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) ta bayar na zaman gida a ranar Litinin a duk yankin kudu maso gabas.
A cewar rahoton, ci gaban ya sa daruruwan abokan cinikin banki sun makale kuma ba sa iya gudanar da ayyukansu.
Wasu daga cikin ma’aikatan bankunan sun ce ma’aikatan hukumar raya babban birnin Owerri ne suka rufe su.
A wani labari na daban, mun ji cewa an nada Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin mamba a kwamitin kawo sauyi a fannin kiwon lafiya wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ke jagoranta.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da kwamitin a ranar Litinin, 6 ga watan Satumba, jaridar The Cable ta ruwaito.
A cewar wata sanarwa da daya daga cikin hadiman shugaba Buhari kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar, an kafa kwamitin ne don ci gaba da aiwatar da gyare-gyare a bangaren.
Asali: Legit.ng