Gwamnan PDP ya samu mukami mai muhimmanci daga Shugaba Buhari
- Muhammadu Buhari ya nada gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin mamba a kwamitin kawo sauyi na fannin kiwon lafiya
- Kwamitin da shugaban kasa ya kaddamar a ranar Litinin yana da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a matsayin shugabanta
- Wasu fitattun likitocin kiwon lafiya kamar Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, suma membobin kwamitin ne
An nada Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin mamba a kwamitin kawo sauyi a fannin kiwon lafiya wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ke jagoranta.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da kwamitin a ranar Litinin, 6 ga watan Satumba, jaridar The Cable ta ruwaito.
A cewar wata sanarwa da daya daga cikin hadiman shugaba Buhari kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar, an kafa kwamitin ne don ci gaba da aiwatar da gyare-gyare a bangaren.
Sauran membobin kwamitin sun hada da Osagie Ehanire, Ministan Lafiya da kuma Shugabannin Kungiyar Likitocin Najeriya (NMA), Kungiyar Magunguna ta Najeriya, kungiyar ma’aikatan jinya da kungiyar gwaje-gwaje ta Najeriya, Vanguard ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gidauniyar Bill & Melinda Gates da Vesta Healthcare Partners za su yi aiki a matsayin masu sa ido a cikin kwamitin.
Shugaba Buhari ya ba Osinbajo shugabancin kwamitin da zai gyara kiwon lafiya a jihohi 36
A baya mun kawo cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa kwamitin da zai fitar da tsare-tsare da dabarun gyara sha’anin kiwon lafiya a Najeriya.
Mai magana da yawun bakin shugaban Najeriyar, Malam Garba Shehu ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar a ranar 6 ga watan Satumba, 2021.
Kamar yadda kuka samu labari a baya, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne zai jagoranci wannan kwamiti da zai yi wannan babban aiki.
Asali: Legit.ng