Saudiyya Kawar Kirki Ce, Ba Zamu Mance da Tallafa Mana da Take Ba, Shugaba Buhari
- Shugaba Buhari ya gana da ministan harkokin waje na ƙasar Saudiya, Yarima Al-Saud a fadarsa dake Abuja
- Buhari ya yaba da kyakkyawar alaƙar dake tsakanin Najeriya da Saudiya wanda ya samo asali shekaru da dama da suka shuɗe
- Yariman ya bayyana cewa ya zo ne ya isar da gaisuwar Sarki Salman, da kuma kara dankon zumunci
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhamadu Buhari, yace ƙasar Saudiya mai ƙarfin tattalin arzikin man Fetur ta kasance mai kirki da mutunta Najeriya.
Shugaban ya faɗi haka ne yayin da ya karɓi bakuncin ministan harkokin waje na ƙasar Saudiyya, Yarima Faisal Bin Farhan Al-Saud, a fadarsa dake Abuja.
Buhari yace duba da yawan al'umma da Najeriya ke da su da kuma ƙarancin manyan ayyukan kasa, yasa ƙasar na bukatar samun kuɗaɗen shiga ta ɓangaren ɗanyen man fetur da take samar wa.
Sabon ministan wuta ga 'yan Najeriya: Kada ku yi tsammanin za a samar da wutan lantarki kamar sihiri
A wani jawabi da kakakin shugaban, Femi Adesina, ya fitar a shafinsa na Facebbok, Buhari yace Saudiya ta kasance mai mutunta Najeriya wajen samar da ɗanyen mai a kasuwar duniya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Buhari yace:
"Saudiyya ta kasance tana mutunta Najeriya ta hanyar rage yawan ɗanyen man da take samar wa domin na kasar mu ya samu shiga a lokuta da dama."
Wace kyakkyawar alaƙa ce tsakanin Najeriya da Saudiyya?
Buhari ya bayyana cewa zumuncin dake tsakanin Najeriya da ƙasar Saudiyya yana da ƙarfi sosai.
Bugu da ƙari shugaban yace yana da kyakkyawar alaƙa da ƙasar Saudiyya tun a baya, a karan kanshi da kuma a gwamnatance.
Sarkin Saudiyya ya aike gaisuwa ga Buhari
A nasa jawabin, Yarima Al-Saud yace ya kawo ziyara ne domin isar da gaisuwa ga Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdul-azeez.
Rahoton Fasaha: Ɓarayi Sun Sace Dalibai 1,409 a Najeriya Cikin Watanni 19, Miliyoyi Sun Salwanta Wajen Fansa
Ministan ya ƙara da cewa masarautar Saudiyya tana jin dadin dangantakarta da Najeriya, "Wanda ya samo asali shekara 61 da suka shuɗe kuma muna son ƙara dangon zumunci."
Ministan yace:
"Ƙasashen biyu suna da kyakkyawar alaƙa a ɓangaren tattalin arziki da kuma siyasa, ba wai tsakanin shugabannin biyu ba kaɗai, harda al'ummarsu."
A wani labarin kuma An Shiga Tashin Hankali a Wata Jami'a Yayin da Malamai Uku Suka Mutu Rana Daya
An shiga yanayin ruɗani da jimami a jami'ar jihar Abia yayin da malaman makarantar uku suka kwanta dama a rana ɗaya.
Rahotanni sun bayyana cewa har yanzun ba'a gano musabbabin mutuwar malaman uku ba, cikinsu harda Farfesa.
Asali: Legit.ng