An Shiga Tashin Hankali a Wata Jami'a Yayin da Malamai Uku Suka Mutu Rana Daya

An Shiga Tashin Hankali a Wata Jami'a Yayin da Malamai Uku Suka Mutu Rana Daya

  • An shiga yanayin ruɗani da jimami a jami'ar jihar Abia yayin da malaman makarantar uku suka kwanta dama a rana ɗaya
  • Rahotanni sun bayyana cewa har yanzun ba'a gano musabbabin mutuwar malaman uku ba, cikinsu harda Farfesa
  • Sai dai wani da ya nemi a sakaya sunasa yace malaman jami'ar na cikin wani hali, domin rabon su da albashi tun watan Janairu

Abia - Jami'ar jihar Abia dake Uturu, ta shiga yanayin tashin hankali da jimami biyo bayan mutuwar lakcarori uku cikin awanni 24, kamar yadda punch ta ruwaito.

Wata majiya daga jami'ar ya bayyana cewa lakcarorin sune, Farfesa A. I. Nwabughuogu na tsangayar tarihi, dakta D. S. Okoroigwe da kuma Dakta Osince Okike na sashin koyar da ilimin siyasa a kimiyyance.

Kara karanta wannan

Bamu yi sulhu da Fulani ba: Yan Irigwe da akewa zargin kashe matafiya a Jos

Rahoto ya nuna cewa har zuwa yanzun ba'a gano musabbabin mutuwar malaman jami'ar ba.

Jami'ar jihar Abia
An Shiga Tashin Hankali a Wata Jami'a Yayin da Malamai Uku Suka Mutu Rana Daya Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wane hali malaman jami'an suke ciki?

Hakanan kuma majiyar ya ƙara da cewa malaman jami'ar sun shiga wani matsanancin hali na rashin kuɗaɗen shiga domin an jima ba'a biyasu albashi ba.

Yace:

"Muna bin bashin albashi na sama da watanni bakwai, karo na karshe da aka bamu haƙƙin mu shine a watan Janairu, 2021."

ASUU Ta tabbatar da mutuwar malaman

Shugaban ƙungiyar malaman jami'o'i ASUU reshen jami'ar jihar Abia, Dakta Victor Nkemdirim, ya tabbatar da mutuwar malaman guda uku.

Shugaban na ASUU ya bayyyana lamarin mutuwar malaman cikin awanni 24 da mara daɗin ji da kuma rashin sa'a.

Duk wani kokari na jin ta bakin kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Abia, Chijioke Nwogu, game da lamarin ya ci tura domin wayarsa ta ƙi shiga.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na kasa: Jigon jam’iyyar ya ce Ali Modu Sheriff ya cancanci jagorantar jam’iyyar mai mulki

Bugu da ƙari har zuwa yanzun da aka rubuta wannan rahoton kakakin yan sandan bai maido da amsar sakonnin karta kwana da aka tura masa ba.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Shiga Ganawa da Shugabannin Tsaro a Fadarsa Aso Villa

Shugaba Buhari ya shiga tattauna da shugabannin tsaron kasar nan a fadarsa dake babban birnin tarayya Abuja.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai hafsoshin soji, sufetan yan sanda da ministoci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: