A daina ba daliban arewa kulawa ta musamman – El-Rufai ga JAMB

A daina ba daliban arewa kulawa ta musamman – El-Rufai ga JAMB

  • Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bukaci hukumar JAMB da ta daina ba daliban arewa fifiko a kan takwarorinsu na kudu
  • El-Rufai ya ce daidaita makin JAMB zai sa daliban arewa zama masu gasa a gida da waje
  • Ya kuma sha alwashin cin galaba kan yan bindiga da 'yan ta'addan da ke addabar jihar

Gwamna Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna ya nemi Hukumar Samar da Guraben Karatu a Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) da ta sanya adadin yawan maki da ake so na ɗaliban arewa su zama daidai da na takwarorinsu na kudu.

El-Rufai, yayin da ya bayyana a wani shirin kai tsaye na Sunrise Daily a gidan talabijin na Channels Television a ranar Litinin, ya bayyana cewa daidaita ma'aunin makin zai sa ɗaliban Arewa su zama masu gasa a cikin gida da ƙasa da ƙasa, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na kasa: Jigon jam’iyyar ya ce Ali Modu Sheriff ya cancanci jagorantar jam’iyyar mai mulki

A daina ba daliban arewa kulawa ta musamman – El-Rufai ga JAMB
El-Rufai ya bukaci hukumar JAMB da ta daina ba 'yan arewa fifiko wajen yanke adadin maki da ake so Hoto: The Guardian
Asali: UGC

El-Rufai ya kuma ce rufe makarantu da aka yi a halin yanzu a jihar shine babban burin 'yan fashi da 'yan ta'adda da ke danne jihar, ya kuma sha alwashin cewa ba za su yi nasara ba, jaridar Punch ta ruwaito.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A kodayaushe Arewa tana baya a fagen ilimi, mun ci gaba da kasancewa yanki marasa galihu tun daga samun ‘yancin kai duk da cewa an ba mu fifiko, a makin JAMB da sauran su. Hakan bai taimaka ba, hasali ma, ya sanya mutanenmu kasala.
“Dangane da wannan banbanci a maki na JAMB da Gwamnatin Tarayya, ina ganin ya kamata a ƙarfafa wa mutane gwiwar yin aiki tukuru da kuma yin gasa sannan kuma a shirye muke mu sanya yaran mu a jihar Kaduna su zama masu gasa, ba a cikin jihar ba kawai, harma a duk duniya.

Kara karanta wannan

Talauci: Rahoto ya nuna 'yan Najeriya miliyan 27 ke samun kudin shiga N100k a shekara

“An rufe makarantu yanzu saboda, bisa shawarar hukumomin tsaro, suna bukatar watanni biyu don gudanar da manyan ayyukan tsaro. Suna yin hakan. Muna da yakinin cewa daga makwanni biyu masu zuwa, za mu fara bude makarantu a hankali.
"Mun kwashe ɗaliban mu da yawa a yankunan karkara waɗanda ba mu da tabbacin za mu iya ba su kariya a makarantun birane, ta haka muna ƙara cunkoso a makarantun birane da za mu iya karewa.
"Ci gaba da rufe makarantu shine ainihin abin da 'yan fashi da' yan Boko Haram ke so kuma ba za mu bari su ci nasara ba amma dole ne mu sanya lafiyar yaran mu da malaman mu a gaba."

Ya kara da cewa za a fara bude makarantun sannu a hankali nan ba da jimawa ba.

A wani labari na daban, gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, yace gwamnatinsa zata duba yuwuwar hana makiyaya kiwon fili a faɗin jihar.

Kara karanta wannan

Sace dalibai 73 a Zamfara: ACF ta dau zafi, ta ce duk gwamnatin da ba za ta kare al’umma ba bata da amfani

Masari ya yi wannan jawabi ne a cikin shirin 'Politics Today' na kafar watsa labarai ta Channels tv ranar Litinin.

Gwamnan ya yi watsi da yadda makiyayan suke yawo daga wannan yankin zuwa wani a faɗin ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel