'Yan bindiga sun afka wa wani gari a Niger, sun sace kaya a shaguna da kuɗaɗen mutane

'Yan bindiga sun afka wa wani gari a Niger, sun sace kaya a shaguna da kuɗaɗen mutane

  • Wasu yan bindiga sun kai hari garin Bassa da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Niger
  • Mazauna garin sun tabbatar da harin inda suka ce maharan sun sace kaya a shaguna da kudade
  • Mazauna garin sun kuma ce akwai yiwuwar maharan 'yan Boko Haram ne domin sun fito daban da sauran maharan da suke zuwa kauyuka

'Yan bindiga sun kai hari garin Bassa da ke ƙaramar hukumar Shiroro na jihar Niger a ranar Laraba, The Cable ta ruwaito.

Muhammad Abdullahi, wani mai sarauta a garin Erene (Gunduma) ya tabbatar da harin a hirar wayan tarho da suka yi a ranar Laraba.

'Yan bindiga sun afka wa wani gari a Niger, sun sace kaya a shaguna da kuɗaɗen mutane
Taswirar Jihar Niger. Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Basarake a garin Bassa ya tabbatar da harin

Abdullahi ya ce ƴan bindigan da ake zargin ƴan Boko Haram ne sun afka garin Bassa a safiyar ranar Laraba kamr yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tubabbun 'yan bindiga sun koma ruwa, sun shiga hannun 'yan sanda a Katsina

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Ban san takamaiman lokacin da suka kawo harin ba amma mun farka da safe mun ji labarin harin. Mun ji cewa maharan sun tsere ne daga Zamfara don su ɓoye a dajin Shiroro bayan jiragen sojojin Nigeria sun musu luguden wuta watanni da suka shuɗe."
"Tun safe ƴan bindiga suka shigo suna lalata shaguna da wasu kaya masu muhimmanci, suna sace abinci da kuɗaɗe. Mun riga mun sanar da ƴan banga na musamman da ke Galkogo (wani ƙauye kusa da Bassa) kuma suna hanyarsu na zuwa garin.
"A halin yanzu da nake maka magana mutane da yawa sun tsere zuwa Erene wasu kuma sun ɓoye a daji. Sun iso a kan babura. Wasu na cewa ƴan Boko Haram ne don sun banbanta da maharan da suka saba kawo hari a ƙauyuka."

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kutsa Gidan Dagajin Ƙauyen Bororo Sun Kashe Shi a Kwara

Abdullahi ya ce maharan sun zo sata ne kawai ya ƙara da cewa ba su kashe kowa ba.

Wani tsohon mazaunin Bassa shima ya tabbatar da harin

A cewar Shehu Nagarta, wani tsohon mazaunin Bassa, yan bindigan sun yi ta cin karen su ba babbaka har zuwa ƙarfe 6 na yamma kafin suka tafi Magami, wani ƙauyen da ke ƙaramar hukumar Shiroro.

Nagarta ya ce yan banga da jami'an tsaro da suka tafi domin ceto mutanen garin ba su dawo ba.

An yi kokarin ji ta bakin yan sanda ko jami'an gwamnati amma hakan bai yi wu ba domin ba su amsa kira da saƙonnin da aka aike musu ba.

Alhaki: Ƴan bindiga 9 sun mutu sakamakon rikici da ya ɓarke tsakanin ɓangarori biyu da basu ga maciji a Kaduna

A wani labarin daban, kun ji cewa kungiyoyi biyu na wasu shu’uman ‘yan bindiga a karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna inda harbe-harbe ya barke tsakaninsu kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Fusatattun Direbobin Keke Nafef Sun Shiga Yajin aiki, Sun Toshe Hanyoyi a Wata Jihar Arewa

Rikicin ya yi sanadiyyar halakar mutane 9 a cikinsu kamar yadda jami’an binciken sirri suka tabbatarwa da gwamnatin jihar Kaduna.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya sanar da hakan a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel