Bayan Datse Sabis, Jiragen Yakin Sojoji Sun Yi Luguden Wuta Kan Sansanonin Yan Bindiga a Zamfara

Bayan Datse Sabis, Jiragen Yakin Sojoji Sun Yi Luguden Wuta Kan Sansanonin Yan Bindiga a Zamfara

  • Sojojin sama da na ƙasa sun yi luguden wuta kan sansanonin yan bindiga a jihar Zamfara
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan gwamnatin jihar ta ɗauki wasu kwararan matakai don magance matsalar tsaro
  • Jiragen yakin sama na sojoji ne suka fara ruwan wuta kan yan tada kayar bayan daga bisani sojin ƙasa suka buɗe wuta kan masu tserewa

Zamfara - Kwanaki ƙalilan bayan gwamnatin Zamfara ta sanar da ɗaukar wasu matakai domin magance ayyukan yan bindiga, sojojin sama da na ƙasa sun yi luguden wuta kan yan bindiga a sansanonin su.

BBC Hausa ta ruwaito cewa Kwamishinan yaɗa labarai, Ibrahim Dosara, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Kwamishinan yace yayin wannan hare-haren ta sama da sojojin Najeriya suka kaddamar kan yan ta'addan, sun kashe wani gawurtaccen ɗan bindiga mai suna, Dan Karami.

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa da Shugaba Buhari, Sanata Ndume Ya Sake Magana Kan Mayakan Boko Haram da Suka Mika Wuya

Jirgin yakin sojojin Najeriya
Bayan Datse Sabis, Jiragen Yakin Sojoji Sun Yi Luguden Wuta Kan Sansanonin Yan Bindiga a Zamfara Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Rahoto ya nuna cewa a baya Ɗan Karami ya taɓa fitar da sakon bidiyo ya bayyana murnarsa bayan sun yi gumurzu da sojoji, kamar yadda punch ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sojojin ƙasa sun buɗe wuta kan masu tserewa

Bugu da kari, sanarwar ta kara da cewa sojojin ƙasa sun buɗe wuta kan ragowar yan bindigan da suka yi kokarin tserewa bayan harin sama.

Rundunar sojojin sama da na kasa sun samu nasara a harin kwantan ɓauna da suka kai ta sama da ƙasa a sansanonin yan tada ƙayar bayan.

Wane matakai gwamnatin Zamfara ta ɗauka?

A baya dai gwamnatin Zamfara, karkashin jagorancin Gwamna Bello Matawalle, ta bada umarnin rufe kasuwanni, tashoshin mota da aka buɗe ba bisa ka'ida ba musamman waɗanda ke gefen titi.

Hakazalika gwamnatin ta bada umarnin datse sabis na sadarwa, wanda hukumomi da kamfanonin sadarwa suka aiwatar cikin gaggawa domin magance matsalar tsaro a jihar ta Zamfara.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun afka ofishin ƴan sandan Zamfara, sunyi kisa, sun sace bindigu AK-47 masu yawa

A wani labarin kuma Gwamnatin Buhari Ta Yi Allah Wadai da Juyin Mulkin da Sojoji Suka Yi a Kasar Guinea

Tawagar sojoji na musamman sun tabbatar da rushe gwamnatin shugaba Alpha Conde tare da tsare shi.

Gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da lamarin tare da kiran a gaggauta dawo da gwamnatin demokaradiyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel