Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC ta sallami shugabanta da ya ce Buhari ya mutu kowa ya huta

Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC ta sallami shugabanta da ya ce Buhari ya mutu kowa ya huta

  • An sallami Alhaji Sulaiman Adamu daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kan kalaman da yayi
  • Adamu, wanda shine shugaban jam'iyyar na Yola yayi wasu kalaman suka kan Buhari
  • Bidiyon Adamu yana zagin Buhari ya fito kwanakin baya a kafafen sada zumunta

Abuja - Kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta kasa ta sallami shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Yola ta Kudu, Alhaji Sulaiman Adamu, daga jam'iyyar.

A jawabin da Sakataren jam'iyyar APC na kasa, John James Akpanudoudehe, ya aikowa Legit.ng, ya ce an sallami Adamu gaba daya daga jam'iyyar.

Ya ce an yanke shawaran hakan ne a zaman jam'iyyar na 16 da akayi ranar Laraba, 1 ga watan Satumba, 2021 a hedkwatar jam'iyyar dake Abuja.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kotu ta kori Gwamna Buni a matsayin shugaban riko na APC, ta dakatar da taron karamar hukuma

Ya kara da cewa kwamitin rikon kwaryan ta tattauna laifukan da Adamu yayi kuma ta duba shawarin da kwamitin bincike kansa suka bada.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jam'iyyar APC ta sallami shugabanta da ya ce Buhari ya mutu kowa ya huta
Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC ta sallami shugabanta da ya ce Buhari ya mutu kowa ya huta Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Laifin me Adamu Sulaiman yayi?

Sulaiman Adamu, ya yi maganganunn batanci kan shugaba Muhammadu Buhari.

Adamu yace da so samu ne, da cutar Korona ta hallaka Buhari mataimakinsa Yemi Osinbajo ya hau kujerarsa.

A cewar majiyoyi, Jigon APCn ya bayyana hakan ne a ganawar wasu manyan masu ruwa da tsaki a jihar, ciki har da tsohon gwamnan Adamawa, Muhammadu Bindow da tsohon Kakakin majalisar jihar Adamawa, Kabiru Mijinyawa.

A faifan bidiyo da DailyNigerian tace ta samu, jigogin APCn sun caccaki shugaba Muhammadu Buhari

Ni fa sulhu kawai naje yi: Tsohon gwamna Bindow ya kare kansa

Biyo bayan kalaman jama'a kan zaman da jigogin APC suka yi idan akayi kalaman suka ga shugaba Muhammadu Buhari, tsohon gwamnan Adamawa, Jibrilla Bindow, ya kare kansa.

Kara karanta wannan

2023: Kungiyar goyon bayan Osinbajo ta fara kamfen na kasa baki daya, ta ziyarci Gwamna Masari na Katsina

Bindow a jawabin da ya saki ta hannun mai magana da yawunsa, Sadiq Abdullateef, Bindow yace ya halarci taron ne matsayin mai sulhu tsakanin bangarorin jigogin APC a Yola ta kudu biyu.

Bindow yace da kyar suka sulhunta bangarorin biyu saboda na caba rikici a zaman shiyasa yayi mamaki da aka hadashi da lamarin sukan Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng