Rikicin cikin gida zai iya tarwatsa mu, Kwankwaso ya ja kunnen shugabannin PDP

Rikicin cikin gida zai iya tarwatsa mu, Kwankwaso ya ja kunnen shugabannin PDP

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ja kunnen shugabannin jam'iyyar PDP kan tsoron tarwatsewar jam'iyyar
  • Ya ce a wannan lokacin, bai dace a ce ana samun rikici ba balle da ba su da shugaban kasa ko gwamnoni masu yawa
  • Tsohon gwamnan ya ce ba shi da lokacin rikici, ya fi mayar da hankali wurin inganta rayuwar jama'a ba neman mulki ba

Kano- Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar PDP ya na iya tarwatsa jam'iyyar baki daya.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Kwankwaso ya ce ba a bukatar irin wannan rikicin a wannan lokacin da jam'iyyar ke fama da rasa mambobin ta.

Rikicin cikin gida zai iya tarwatsa mu, Kwankwaso ya ja kunnen shugabannin PDP
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ja kunnen shugabannin PDP. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A yayin zantawa da BBC Hausa, Kwankwaso ya ce tuni ya nisanta kan sa daga dukkan wani rikici kuma kamar yadda ya ce, wadanda ba kwararrun 'yan siyasa ba ne suka hura wutar.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na kasa: Jigon jam’iyyar ya ce Ali Modu Sheriff ya cancanci jagorantar jam’iyyar mai mulki

"A yanzu karfin jam'iyyar ya ragu kuma a karshe abinda zai faru shi ne za mu tarwatse baki daya."
"Ka ga wannan sakamakon ba zai taimake mu ba saboda ba mu da shugaban kasa kuma ba mu da gwamnoni masu yawa," Kwankwaso ya ce.

Ya shawarci shugabannin jam'iyyar da su mayar da hankali kan jama'arsu da yadda za su taimake su.

"Mutum kamar ni ba shi da wata alaka da rikici. Ni ina duban abinda zai kawo ci gaba ne ga jama'a, abinda kowanne shugaba na gari zai mayar da hankali a kai."
“Shugaban jam'iyya yanzu wata daya ya rage masa. A tunani na, zai fi idan ya tsaya ta yadda za mu bayyana da karfinmu.
“Amma wannan rikicin na habaka ne da taimakon wadanda suke son shugabanci. Ba don damuwar jama'a su ke yi ba," ya kara da cewa.

Kara karanta wannan

Bagudu: Muguntar 'yan bindiga ta fi shafar Fulani, ba mu sauraron labaransu ne kawai

'Yan sanda sun bindige Buba Baromi, kasurgumin mai kai wa 'yan bindiga bayanai a Niger

A wani labari na daban, jami'an rundunar yaki da 'yan bindiga ta 'yan sandan jihar Niger sun bindige gagararren mai kai wa 'yan bindiga bayanai, Buba Baromi. An sheke Baromi ne a wata maboyarsa da ke dajin Damba na jihar Niger, PRNigeria ta ruwaito.

PRNigeria ta tattaro cewa, wasu mafarautan yankin sun jagoranci 'yan sanda maboyar Baromi inda ya ke jinyar wani harbin bindiga da aka yi masa yayin wata arangama da yayi da jami'an tsaro a baya.

Wani jami'in sirri da aka yi aikin da shi, ya sanar da PRNigeria cewa, Baromi ba bayanai kadai yake kai wa 'yan bindiga ba, har jagorantarsu yake yi zuwa wurin da za su kai farmaki kuma su sace jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng