Da dumi-dumi: Kotu ta kori Gwamna Buni a matsayin shugaban riko na APC, ta dakatar da taron karamar hukuma

Da dumi-dumi: Kotu ta kori Gwamna Buni a matsayin shugaban riko na APC, ta dakatar da taron karamar hukuma

  • An umarci gwamna Buni na jihar Yobe da ya daina nuna kansa a matsayin shugaban riko na jam'iyyar APC har sai an yanke hukunci kan karar da aka shigar a kansa
  • Wata babbar kotu a Asaba, jihar Delta, ta bayar da umurnin biyo bayan wani tsohon kara da wasu fusatattun manyan jiga-jigan jam'iyyar APC suka gabatar
  • Kotun ta kuma dakatar da jam’iyya mai mulki ta APC daga ci gaba da babban taronta na kananan hukumomi da aka shirya yi a ranar 4 ga watan Oktoba, 2021

Asaba, jihar Delta - Rahotannin da ke fitowa sun nuna cewa wata babbar kotu da ke zaune a Asaba, babban birnin jihar Delta, ta dakatar da taron karamar hukuma na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da aka shirya yi ranar 4 ga Oktoba, 2021.

Kara karanta wannan

Hoton Mutumin Da Kotu Ta Yanke Wa Hukuncin Ɗaurin Gidan Yari Bayan An Kama Shi Yana Satar Doya

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kotun ta kuma hana Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe daga daukar kansa a matsayin shugaban riko na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) har sai an yanke hukunci.

Da dumi-dumi: Kotu ta kori Gwamna Buni a matsayin shugaban riko na APC, ta dakatar da taron kananan hukumomi
An umarci gwamna Buni na jihar Yobe da ya daina nuna kansa a matsayin shugaban riko na jam'iyyar APC Hoto: Mai Mala Buni Media
Asali: Facebook

A cewar The Guardian, mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Olorogun Elvis Ayomanor, wanda ya jagoranci wasu jami’an jam’iyyar APC na Delta, ya garzaya kotu biyo bayan babban taron mazabu na ranar 10 ga watan Yuli, 2021, wanda ake zargin an janye.

A cikin tsohon kudirin da masu karar suka shigar, babban lauyan, Ebipade Richard, ya roki kotun da ta ba da sassaucin maki bakwai da ake nema.

Richard ya kara da cewa ci gaba da babban taron karamar hukumar a jihar Delta zai haifar da illa ga wadanda yake karewa.

Kara karanta wannan

Da dumi: Kotu ta soke dakatarwar da aka yi min a matsayin Shugaban APC, Oshiomhole ya bayyana mataki na gaba

Kwanaki bayan ganawa da Tinubu, shahararren gwamnan APC ya magantu akan kudirin takarar shugaban kasa

A wani labari, Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya nisanta kansa daga ayyukan da ke alakanta shi da zaben shugaban kasa na 2023.

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa gwamnan na Ondo ya bayyana ci gaban a matsayin wani yunkuri na jan hankali mara amfani.

Legit.ng ta tattaro cewa matsayin Akeredolu yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Richard Olatunde ya fitar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel