Da Dumi: Buni ya yi martani kan korarsa da aka yi a matsayin shugaban APC, ya ce umurnin Kotu ba a kansa bane

Da Dumi: Buni ya yi martani kan korarsa da aka yi a matsayin shugaban APC, ya ce umurnin Kotu ba a kansa bane

  • Shugaban riko na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Mai Mala Buni, ya mayar da martani kan umarnin kotu da ta sallame shi
  • Wata babbar kotu da ke zama a Asaba, babban birnin jihar Delta a ranar Laraba, 1 ga watan Satumba, ta dakatar da shi daga aiki a matsayin shugaban APC
  • Jam’iyya mai mulki ta fada cikin rikici kan halaccin kasancewar Gwamna Buni a matsayin shugaban jam’iyyar APC

Damaturu, Yobe - Shugaban kwamitin tsare-tsaren babban taro (CECPC) na Jam'iyyar APC mai mulki kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya mayar da martani kan korarsa.

Vanguard ta rahoto cewa umarnin da babbar kotun jihar Delta da ke Asaba ta bayar a ranar Laraba, 1 ga watan Satumba, ta hana Buni aiki a matsayin shugaba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kotu ta kori Gwamna Buni a matsayin shugaban riko na APC, ta dakatar da taron karamar hukuma

Da Dumi: Buni ya yi martani kan korarsa da aka yi a matsayin shugaban APC, ya ce umurnin Kotu ba a kansa bane
Buni ya yi martani kan korarsa da aka yi a matsayin shugaban APC, ya ce umurnin Kotu ba a kansa bane Hoto: APC
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa ya bayyana cewa wannan umurnin ba a kansa bane a matsayinsa na shugaban riko na jam'iyyar APC na kasa.

Gwamnan ya yi magana ne ta cikin wata sanarwa da babban daraktansa na harkokin yada labarai, Mamman Mohammed, ya fitar a ranar Alhamis, 1 ga watan Satumba a Abuja.

Ya ce makirai ne kawai ke fassara umarnin a baibai domin umurnin a kan shugaban riko na jihar Delta ne ba a kan shi, Buni ba.

Jawabin ya ce:

“Mista Elvis Ayomanor da wasu mutane bakwai a ranar 19 ga watan Agusta sun shigar da karar APC da shugabancinta a wata babbar kotun shari’a, Asaba, jihar Delta, inda suke kalubalantar sakamakon babban taron jam’iyyar na mazabu na ranar 31 ga watan Yuli, 2021.

Kara karanta wannan

An yi cece-kuce yayin da shugabar karamar hukuma ta rabawa manoma tallafin fatanya, adda da doya guda

“Masu karar sun kuma nemi kotu ta ba da umarni na wucin gadi don hana shugaban da mambobin kwamitin rikon kwarya daga yin aiki ko gabatar da kansu a matsayin jagororin jam’iyyar har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan karar da aka shigar a gaban kotu kan babban taron mazabar a jihar Delta."

Kotu ta kori Gwamna Buni a matsayin shugaban riko na APC, ta dakatar da taron karamar hukuma

A baya mun kawo cewa wata babbar kotu da ke zaune a Asaba, babban birnin jihar Delta, ta dakatar da taron karamar hukuma na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da aka shirya yi ranar 4 ga Oktoba, 2021.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kotun ta kuma hana Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe daga daukar kansa a matsayin shugaban riko na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) har sai an yanke hukunci.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: An yi gagarumin sauyi a majalisar Shugaba Buhari, an sallami ministoci 2 daga arewa

A cewar The Guardian, mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Olorogun Elvis Ayomanor, wanda ya jagoranci wasu jami’an jam’iyyar APC na Delta, ya garzaya kotu biyo bayan babban taron mazabu na ranar 10 ga watan Yuli, 2021, wanda ake zargin an janye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng