Da dumi-dumi: Shugaban APC da aka kora ya magantu kan sallamarsa daga jam'iyyar, yayi magana akan komawa PDP

Da dumi-dumi: Shugaban APC da aka kora ya magantu kan sallamarsa daga jam'iyyar, yayi magana akan komawa PDP

  • Tsohon shugaban jam'iyyar APC a karamar hukumar Yola ta Kudu, Sulaiman Adamu, ya mayar da martani kan korarsa daga jam'iyyar
  • Adamu ya ce duk da cewa jam'iyyar ba ta sanar da shi a hukumance ba, amma ya amince da korar a matsayin nufin Allah
  • Tsohon jigon na APC ya kuma bukaci magoya bayansa da kada su fice daga APC kamar yadda shi ma ya yi watsi da sauya shekarsa zuwa jam'iyyar adawa ta PDP

Yola, jihar Adamawa - Sulaiman Adamu, shugaban jam’iyyar APC da aka kora a karamar hukumar Yola ta kudu, ya roki magoya bayansa da su ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyya mai mulki.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Adamu a ranar Alhamis, 2 ga watan Satumba ya bayyana korarsa daga APC a matsayin nufin Allah wanda yake karba da zuciya daya.

Kara karanta wannan

Da Dumi: Buni ya yi martani kan korarsa da aka yi a matsayin shugaban APC, ya ce umurnin Kotu ba a kansa bane

Da dumi-dumi: Shugaban APC da aka kora ya magantu kan sallamarsa daga jam'iyyar, yayi magana akan komawa PDP
Sulaiman Adamu, shugaban APC da aka kora a karamar hukumar Yola ta kudu, ya bukaci magoya bayansa da su ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyya mai mulki. Hoto: Thebellng, Hon Mai Mala Buni
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa Adamu, ya ce har yanzu jam'iyyar ba ta sanar da shi hukuncinta a hukumance ba.

Kada ku yi tsammanin zan shiga PDP - Adamu

Duk da fitarsa daga APC, Adamu ya ce kada wanda ya sa ran zai koma jam'iyyar adawa ta PDP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, bai taba zama mamba a kowace jam’iyya ba in banda APC.

Kalamansa:

“Na yarda da kaddara ta. Ina ganin shi a matsayin nufin Allah. Abin da na taba so shi ne APC ta ci gaba da kasancewa a kan mulki kuma hakan na iya tabbatar da nasarar da muka samu a zabe.”

Ya kara da cewa:

“Za a yi zabe, ina da katin zabe na, daidai. Akalla, ba su cire min wannan ba. Domin ban taba zama memba na wata jam’iyyar siyasa ba sai APC. Don haka, kada ma ku yi tsammanin zan koma PDP. ”

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kotu ta kori Gwamna Buni a matsayin shugaban riko na APC, ta dakatar da taron karamar hukuma

An kori Adamu ne sakamakon kalaman batanci da ya yi wa Shugaba Buhari. Sai dai tsohon jigon na APC ya musanta wannan magana, kamar yadda Daily Independent ta ruwaito.

Jam'iyyar APC ta sallami shugabanta da ya ce Buhari ya mutu kowa ya huta

A baya Legit.ng ta rahoto cewa kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta kasa ta sallami shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Yola ta Kudu, Alhaji Sulaiman Adamu, daga jam'iyyar.

A jawabin da Sakataren jam'iyyar APC na kasa, John James Akpanudoudehe, ya aikowa Legit.ng, ya ce an sallami Adamu gaba daya daga jam'iyyar.

Ya ce an yanke shawaran hakan ne a zaman jam'iyyar na 16 da akayi ranar Laraba, 1 ga watan Satumba, 2021 a hedkwatar jam'iyyar dake Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng