'Yan majalisar Nasarawa 3 sun tsallake rijiya da baya akan hanyarsu ta zuwa jana’iza
- Wasu mambobin majalisar dokokin jihar Nasarawa uku sun tsallake rijiya da baya a hannun 'yan bindiga da suka kusa aika su lahira
- 'Yan majalisar sun yi gamo da maharan ne a lokacin da suke hanyarsu ta komawa garin Lafia, bayan sun halarci jana’iza a Karamar Hukumar Akwanga ta jihar
- Lamarin ya afku ne a safiya ranar Laraba, 1 ga watan Satumba
Nasarawa - 'Yan majalisar dokokin jihar Nasarawa uku sun tsallake rijiya da baya a ranar Laraba, 1 ga watan Satumba, inda suka tsere daga wani "yunƙuri na kashe su" a kan babbar hanyar Akwanga zuwa Lafiya.
Jaridar Newswirengr ta kuma ruwaito cewa ‘yan majalisar wadanda suka hada da Hon Samuel Tsebe (APC-Akwanga ta Kudu), Hon David Maiyaki (APC- Karu / Gitata) da Hon Peter Akwanga (PDP- Obi 1), suna kan hanyarsu ta zuwa jana’iza ne lokacin da lamarin ya afku.
Mai magana da yawun Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Jibrin Gwamna, ya ce:
“’Yan majalisar na hanyarsu ta dawowa daga jana’izar matar dan uwan Honorabul Tsebe ne lokacin da maharan suka bude wa motar Honorabul Tsebe wuta a kauyen Wowyen da ke hanyar Akwanga zuwa Lafia.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa ana zargin Honorabul Samuel Tsebe ne aka so hallakawa, saboda motocin ’yan majalisar su uku sun yi jerin gwano, amma tasa ce a karshe kuma ita aka bude wa wuta.
Da yake ba da labarin irin wahalar da suka sha, Hon Tsebe ya ce:
“Lokacin da muke gabatowa kauyen Wowyen da ke kan hanyar Akwanga / Lafia, tsakanin Kwalejin Horar da ‘Yan sanda, Ende Hills da ƙauyen ta bangaren gada.
“Na ji karar harbin bindiga a gefen direba a motata kuma ni nake tuki. Harsashi ya fasa gilashin motata, don haka wannan ya sa nake zargin wani na bibiyar shige da ficena kuma ya san ni nake tuki.
“Yunkurin ’yan ina-da-kisa ne kuma na sanar ’yan sanda abin da ya faru.
“Muna godiya ga Allah da Ya tseratar da mu."
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai da dama a wata makaranta a jihar Zamfara
A wani labari kuma, mun ji cewa wasu ‘yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai farmaki wata makaranta da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara.
An tattaro cewa maharan sun kuma yi awon gaba da wasu dalibai da dama a makarantar wacce take ta maza da mata a hade.
Asali: Legit.ng