Cikar Najeriya shekaru 61: FG ta kafa kwamitin mutum 12 domin shirye-shirye
- Gwamnatin tarayya ta rantsar da kwamitin mutum 12 na shirya shagalin cikar Najeriya 61 da samun 'yancin kai
- Kamar yadda sakataren gwamnatin tarayya, SGF Boss Mustapha ya ce an fara shirin da wuri ne domin a samu bikin ya tafi daidai
- Za a fara da addu'o'in zaman lafiya a masallacin kasa da babbar majami'ar kasa kafin a yi fareti kafin a rufe da taron bada kambun yabo
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta rantsar da kwamitin mutane 12 da suka hada da ministoci domin tsara yadda shagalin bikin cika murnar shekaru 61 da samun 'yancin kan kasa.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa Najeriya za ta cika shekaru 61 a ranar 1 ga watan Oktoba.
A yayin rantsar da kwamitin a ranar Alhamis a Abuja, sakataren gwamnatin tarayya, SGF Boss Mustapha, ya ce hikimar nan ta biyo bayan bukatar fara shirin shagalin da wuri domin samun sakamako mai kyau, Premium Times ta ruwaito.
Hikimar haka ita ce a fara shirin. Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana son amfani da kudi kadan domin samun sakamako mai kyau.
Kwamitin da ke karkashin shugabancin SGF, ya kunshi ministan yada labarai, ministan cikin gida, ministan babban birnin tarayya, ministan hannayen jari, cinikayya da masana'antu, ministan lafiya tare da sifeta janar na 'yan sanda, darakta janar na DSS.
Premium Times ta wallafa cewa, sauran sun hada da: Kwamanda, Guard Birgade, babban sakataren gwamnati, ofishin kula da masallacin kasa da tsaron fadar shugaban kasa da sauransu.
Shagulgulan da ake so a yi a bikin zagayowar ranar samun 'yancin kasa kamar yadda SGF ya sanar sun hada da kammala shagalin cikar kasa shekaru 60 da samun 'yanci.
Za a yi addu'a a babbar majami'ar kasa a ranar da babban Masallacin kasa a ranar 26 ga watan Satumba da kuma liyafar dare ta bada kambun jinjina a ranar Lahadi, 3 ga watan Oktoba.
Jawabi ga 'yan kasa da kuma faretin tunawa da ranar samun 'yancin kai za a yi shi a babban filin wasa na Eagle Square a ranar Juma'a 1 ga watan Oktoba," SGF Boss yayi bayani.
Hakazalika, Niyi Adebayo, wanda shine ministan hannayen jari, cinikayya da masana'antu, ya sanar da cewa babu shakka kwamitin zai tabbatar da nasarar ayyukansu.
Zamfara: Ƴan bindiga sun sheƙe rai 1, sun tasa keyar 7 kan ƙin biyan haraji
A wani labari na daban, miyagun 'yan bindiga sun sheke mutum 1 kuma sun tasa keyar mutum bakwai a kauyukan Dadah, Tukurawa da Gandamasu a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
Premium Times ta ruwaito cewa, miyagun 'yan bindigan sun kai farmaki kauyukan a daren Alhamis sakamakon kin biyan haraji da mazauna kauyen suka yi wanda 'yan bindigan suka kallafa musu.
Zurmi tana daya daga cikin kananan hukumomi a jihar Zamfara da 'yan bindiga suka gallaba. Suna da iyakoki da karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.
Asali: Legit.ng