Bayan da Taliban ta karbe mulkin Afghanistan, Amurka ta kai hari da jirgi
- Amurka ta kai hari kan wani mutum da ta yi zargin dan kunar bakin wake ne a Afghanistan
- Wannan na zuwa ne bayan kwanaki kadan da aka samu wata fashewa a filin jirgin Kabul
- Rahoto ya bayyana cewa, mutane uku sun mutu ciki har da mace da kuma yaro karami
Afghanistan - Sojojin Amurka sun kai hari da jirgi mara matuki kan wani mutum da ta ce mai shirin kunar bakin wake ne na ISIS-K a lardin Nangarhar da ke gabashin Afghanistan, a yayin da ake gargadin yiwuwar kai sabbin hare-hare wajen kokarin kwashe Amurkawa daga Kabul.
Manufar yunkurin jigilar kwashe Amurkawa da 'yan Afghanistan wadanda suka taimaka wa sojojin Amurka da jami'ai daga kasar zuwa karshen watan nan ya zo karshe.
A cewar mazauna yankin da aka kai harin a daren Juma'a, akalla mutane uku sun mutu - namiji, mace da yaro - kuma mutane da dama sun jikkata.
Kungiyar ISIS-K Amurka ta nufi kai wa hari
Sai dai, a bangare guda, Ma'aikatar Tsaro ta Amurka ta ce a cikin wani takaitaccen bayani ranar Asabar cewa an kashe manyan 'yan kungiyar ISIS-K (Islamic State- Khorasan) guda biyu a harin, yayin da aka jikkata wani guda.
Amurka ta ce babu wani adadi na fararen hula da aka rasa a harin, in ji Manjo Janar William “Hank” Taylor, Mataimakin Daraktan Hadin Gwiwar Ma’aikatan Yankuna, a ranar Juma’a.
Bidiyo na musamman da hirarrakin da CNN ta samu kai tsaye daga manema labarai na kasar Afganistan a wurin, ya nuna dan karamin tasiri gami da lalacewar bangon da ke kewaye da ginin da aka buga da kuma wasu abubuwan dake wajen.
A cewar rahoton Reuters, wannan hari shi ne na biyu da sojojin Amurka suka kai tun bayan harin kunar bakin wake da kungiyar IS ta kai a wajen filin jirgin sama ranar Alhamis ta kashe sojojin Amurka 13 da fararen hula da dama na Afghanistan.
An yi imanin cewa mutumin da aka kai wa harin da jirgi mara matuki "yana da alaka da yiwuwar kai hari a filin jirgin sama," kamar yadda wani jami'in tsaron Amurka ya shaida wa CNN ranar Asabar.
Taliban ta haramta kida a Afghanistan, an sanya wa mata sabuwar doka
A wani labarin, Kungiyar Taliban ta bayyana cewa za ta tabbatar da haramta kida a Afghanistan saboda "Ba Musulunci ba ne".
Wannan batu na kunshe ne a cikin wata hira da jaridar New York Times da kakakin kungiyar Taliban, Zabiullah Mujahid, a ranar Alhamis 26 ga watan Agusta, Ripples Nigeria ta ruwaito.
Sai dai ya lura cewa Taliban na fatan shawo kan mutane su yi biyayya ga sabuwar dokar, maimakon tilasta musu.
Asali: Legit.ng