FG Ta Fara Rabawa Talakawa Masu Karamin Karfi N20,000, Ta Bayyana Rukunin Mutanen da Zasu Amfana

FG Ta Fara Rabawa Talakawa Masu Karamin Karfi N20,000, Ta Bayyana Rukunin Mutanen da Zasu Amfana

  • Gwamnatin tarayya ta fara biyan hakkokin yan Najeriya da suka amfana da shirin tallafi na CCT
  • Shugabar sashin shirin reshen jihar Kogi, Mrs Falilat Abdurasaq, tace an fara biyan N20,000 na tsawon wata huɗu
  • Tace wannan na daga cikin kokarin da gwamnatin shugaba Buhari take na tsamo talakawa miliyan 100m daga talauci

Kogi - Gwamnatin tarayya ta fara biyan tallafin N20,000 ga mutane 74,000 a jihar Kogi, waɗanda aka tantance karkashin shirin CCT, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Gwamnati ta kirkiro shirin CCT (Conditional Cash Transfaer) ne domin bada tallafin N5,000 ga magidanta masu karamin karfi karkashin tsarin NSIP a ma'aikatar jin kai da walwala.

Shugaban sashin shirin na CCT a jihar Kogi, Mrs Falilat Abdurasaq, itace ta faɗi haka wurin da aka ware domin biyan kudin dake Abocho, karamar hukumar Dekina, jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Cikar Najeriya shekaru 61: FG ta kafa kwamitin mutum 12 domin shirye-shirye

FG fara biyan yan Najeriya da suka amfana da shirin CCT
FG Ta Fara Rabawa Talakawa Masu Karamin Karfi N20,000, Ta Bayyana Rukunin Mutanen da Zasu Amfana Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Premium times ta ruwaito shugabar na cewa wannan tallafin na cikin kokarin da gwamnati ke yi na cika kudirin shugaba Buhari na ceto yan Najeriya miliyan 100m daga ƙangin talauci.

Yaushe aka fara bada tallafin?

Mrs AbdulRazak tace

"am fara biyan kuɗaɗen tun ranar Alhamis da ta gabata, kuma zuwa yanzun waɗanda zasu amfana akalla 7,000 sun amshi N20,000 a faɗin karamar hukumar Dekina."

Ta kara da cewa N20,000 sune tallafin da gwamnati ta yi alkawarin ba su na N5,000 duk wata daga Janairu, zuwa Afrilu.

A cewar Abdulrazak, duka kananan hukumomi 21 na Kogi sun fara dara wa da wannan tallafin kuma zasu cigaba amfana har zuwa sanda za'a kammala.

Me shirin CCT ya kunsa?

Mrs Abdurasaq ta jaddada cewa an kirkiri shirin tallafi na CCT ne domin talakawa kadai kuma domin a fitar da su daga cikin kangin talauci.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An harbe mutum 11 har lahira a sabon harin da aka kai Katsina

Ta kara da cewa shirin ya canza rayuwar baki ɗaya waɗanda zasu amfana ta hanyar horas wa ta musamman da aka ba su.

A jawabinta tace:

"Mutanen da muka horar a wannan shirin sun koyi ɗabi'ar tattalin kudi, kuma sun shiga irin asusun nan da ake na adashe kamar Ojo da Isusu."
"Hakazalika sun samu kwarewa kan abubuwan da aka koya musu ɗaya bayan ɗaya da kuma a cikin rukuni-rukuni.

Daga nan kuma ta yi kira ga mutanen da suka amfana da tallafin su tabbata sunyi amfani da kuɗin ta hanyar da ta dace kuma su cigaba da zuwa wurin horo da karɓar shawarwari.

A wani labarin kuma Bayan Shekaru 30, Jihar Mu Ta Fi Kowace Jiha Zaman Lafiya a Najeriya, Gwamna Bello

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, ya yi ikirarin cewa jiharsa ta fi kowace jiha zaman lafiya a faɗin Najeriya.

Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da yake jawabi ga mutanen jihar a wani ɓangare na bikin murnar cika shekara 30 da kafuwa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotu Ta Maida Uche Secondus Mukaminsa Na Shugaban Jam'iyyar PDP

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262