Da dumi-dumi: Yan majalisar Anambra na jam'iyyar APGA guda 6 sun sauya sheka zuwa APC gabanin zaben gwamna

Da dumi-dumi: Yan majalisar Anambra na jam'iyyar APGA guda 6 sun sauya sheka zuwa APC gabanin zaben gwamna

  • Gabanin zaben gwamna na ranar 6 ga watan Nuwamba, a jihar Anambra, jam’iyyar APC ta sake samun karfi
  • Wasu ‘yan majalisar jihar shida daga jam’iyyar APGA sun sauya sheka zuwa APC
  • Tuni aka gabatar masu da tutar jam’iyyar mai mulki a wani taro da aka yi cikin sirri

Awka, Anambra - Karfin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben gwamnan Anambra da za a gudanar a ranar 6 ga watan Nuwamba ya samu tagomashi a daren ranar Talata lokacin da 'yan majalisar dokoki shida karkashin All Progressives Grand Alliance (APGA) suka koma APC.

Shugaban Kwamitin rikon kwarya na APC kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya karbi 'yan majalisar tare da gabatar masu da tutar APC cikin gaggawa a karshen taron dabarun da aka yi a cikin sirri, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Kungiyar goyon bayan Osinbajo ta fara kamfen na kasa baki daya, ta ziyarci Gwamna Masari na Katsina

Da dumi-dumi: Yan majalisar Anambra na jam'iyyar APGA guda 6 sun sauya sheka zuwa APC gabanin zaben gwamna
Yan majalisar Anambra na jam'iyyar APGA guda 6 sun sauya sheka zuwa APC gabanin zaben gwamna Hoto: APC
Asali: Facebook

‘Yan majalisan shida su ne: Hon. Nonso Okafor mai wakiltar Nnewi ta Arewa; Hon. Timothy Ifedioramma mai wakiltar Njikoka 1; Hon. Cater D. N Umeoduagu mai wakiltar Aguata 1.

sauran sune Hon. Lawrence Ezeudu mai wakiltar Dumekofia; Hon. Arthur Chiekwu mai wakiltar Idemmih North da Hon. Edward Ibuzo, mai wakiltar Onisha North 2.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake karbar wadanda suka sauya shekar a wani dan takaitaccen biki a yammacin Talata a Abuja, Mai Mala Buni ya sake jaddada kudirin jam’iyyar na lashe zaben gwamnan Anambra, wanda ya sa himma wajen shigar da masu ruwa da tsaki a jihar Anambra.

Buni ya ce:

"Ina kallon abin da ke faruwa, musamman yanzu da fitattun 'yan majalisar jihar suka fara dawowa jam’iyyar, an samu ci gaba kuma mutanen Anambra suna komawa APC."

Daga bisani shugaban jam’iyyar ya baiwa ‘yan majalisar tutar APC a karshen wani taron dabarun da aka yi a cikin sirri.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan sanda sun yi nasarar kasha Shugaban IPOB/ESN a kudu maso gabas

Wadanda suka sauya shekar sun bayyana APC a matsayin wacce aka fi so kuma sun yi alkawarin tattara magoya baya don samun nasara a zaben gwamna na ranar 6 ga Nuwamba.

Da yake nasa jawabin, gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya ce mutanen kudu maso gabas sun farka kuma yankin ya jajirce kan siyasar kasa kuma ya kasance wani bangare na Najeriya.

Ya kuma nuna kwarin gwiwa cewa jam’iyyarsa za ta lashe zaben gwamnan jihar Anambra, jaridar Leadership ta ruwaito.

'Yan APC sun roki Buhari ya mika kujerarsa zuwa kudancin Najeriya a zaben 2023

A wani labari, wata kungiya a jam'iyyar APC mai suna South East Mandate (SEM), ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya saukaka hanyoyin zabar dan takarar shugaban kasa daga amintattun mambobin jam’iyyar na Kudu maso Gabas a zaben 2023.

Ta ce manufarta ita ce tabbatar da an samu shugaba daga yankin na Kudu maso Gabas a matsayin wanda zai gaji Shugaba Buhari, Daily Sun ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Sanata Stella Oduah ta sauya sheka daga PDP zuwa APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel